Coronavirus: Yadda garkuwar jiki ke yakar cutar

Researcher at a German pharmaceutical company demonstrates workflow testing for Covid-19 research.

Asalin hoton, EPA

Masana kimiyya a Australia sun ce sun gano yadda garkuwar jiki take yakar kwayar cutar Covid-19.

Sakamakon bincikensu da suka wallafa a mujallar kimiyya ta Nature Medicine ranar Talata, ya nuna mutane na murmurewa daga coronavirus kamar yadda suke warwarewa daga mura.

Masanan sun ce sun gano kwayar halittar da ke zame wa mutum garkuwar jiki kuma hakan zai taimaka wajen samar da riga-kafin cutar coronavirus.

A fadin duniya, hukumomi sun tabbatar cewa fiye da mutum 160,000 suka harbu da coronavirus kuma kusan mutum 6,500 sun mutu.

"Wannan bincike yana da muhimmanci saboda shi ne karon farko da za mu fahimci yadda garkuwar jikinmu take yakar coronavirus," a cewar daya daga cikin masanan da suka yi binciken, Farfesa Katherine Kedzierska.

Masana sun jinjina wa Cibiyar Bincike kan cututtuka masu yaduwa ta Melbourne's Peter Doherty Institute for Infection and Immunity, inda wani masani ya ce hakan "gagarumin ci gaba" ne.

Me aka gano?

Mutane da dama sun samu sauki daga Covid-19, abin da ke nufin garkuwar jiki za ta iya yakar cutar.

Sun gano su ne ta hanyar sanya ido sosai kan wata mai fama da cutar, ko da yake bata ci karfinta ba amma dai a baya bata yi fama da matsalolin rashin lafiya ba.

Matar mai shekara 47 'yar asalin birnin Wuhan da ke China, ta je wani asibiti a Australia. Ta samu sauki bayan kwana 14.

Farfesa Kedzierska ta shaida wa BBC tawagarta ta yi bincike kan "dukkan rawar da garkuwar jikin za ta taka" wajen kare mai fama da cutar.

Kwana uku kafin matar ta soma murmurewa, an gano wasu kwayoyin halitta a cikin jininta. Kazalika an gano irin wadannan kwayoyin a jinin masu fama da mura a daidai wannan lokaci, a cewa Farfesa Kedzierska.

Hoton kirji ya nuna yadda makogwaron mai fama da cutar ke washewa bayan kwayoyin haliyyar da ke garkuwa sun bayyana

Asalin hoton, PETER DOHERTY INSTITUTE

Bayanan hoto, Hoton kirji ya nuna yadda makogwaron mai fama da cutar ke washewa bayan kwayoyin haliyyar da ke garkuwa sun bayyana

Ta gaya wa BBC cewa "Mun yi matukar farin ciki game da sakamakon - ganin cewa za mu iya gano kwayoyin halitta masu yin garkuwa a jikin mutumin da ke fama da cutar tun ma kafin mu samu ci gaba a fannin lafiya."

Masana fiye da sha biyu ne suka yi aiki babu dare babu rana tsawo mako hudu domin gudanar da wannan bincke, in ji ta.

Tayaya hakan zai taimaka?

Gano yadda kwayoyin halitta masu garkuwa ke fitowa ka iya taimakawa "wajen gano yadda cutar ke yaduwa", a cewar Farfesa Bruce Thompson, shugaban tsangayar kimiyya a Jami'ar Fasaha ta Swinburne.

"Idan ka san lokacin da kwayoyin halittar ke mayar da martani ga cuta za ka yi hasashen a matakin da kake wurin warkewa daga cutar," in ji Farfesa Thompson a hirarsa da BBC.

Ministan Lafiya na Australia Greg Hunt ya ce binciken zai taimaka wurin "hanzarta" samar da riga-kafin coronavirus da kuma irin magungunan da za a bai wa mai fama da ita.

Bayanan bidiyo, Yadda masana ke bincike don gano riga-kafin coronavirus

Farfesa Kedzierska ta ce matakin da za su dauka nan gaba shi ne na koarin gano dalilan da suke sanya wa kwayoyin da ke garkuwar ba sa aiki sosai idan cutar ta yi tsanani.

"Yana da matukar muhimmaci yanzu mu fahimci abin da aka rasa ko kuma bambancin da aka samu kan mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ko kuma wadanda suke tsananin fama da cuta - ta yadda za mu kare su," in ji ta.