Ganduje ya nada Aminu Ado Bayero sabon sarkin Kano

An nada Aminu Ado sabon sarkin Kano.

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a gidan gwamnati ranar Litinin, jim kadan bayan sauke Sarki Sanusi II.

Gabanin nadin nasa shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi da Gwamna Ganduje ya kirkira a shekarar 2019.

Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.

Ya rike mukamai da dama a Masarautar Kano da suka hada da Turakin Kano da Sarkin Dawakin Tsakar Gida da kuma Wamban Kano.

Shi ne da na biyu babba a maza ga marigayi Sarki Ado Bayero.

Karin labarai masu alaka