Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An samu mutum na biyu da ya kamu da coronavirus a Najeriya
An samu mutum na biyu da ya kamu da coronavirus a Najeriya.
Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter a ranar Litinin da misalin karfe 10.30 na safe.
NCDC ta ambato minsitan lafiya na kasar yana mai tabbatar da samun mutum na biyu mai dauke da cutar ta Covid19 a kasar.
An gano mai dauke da cutar ne a jihar Ogun cikin mutanen da aka killace kwanakin baya, "kuma an gano cutar a jikinsa ne a kokarin da muke na gano duk wadanda suka yi alaka da mai dauke da cutar na farko dan kasar italiya."
NCDC ta ce mutumin na biyu ba shigo da cutar ya yi kasar ba "amma ya yi mu'amala da dan Italiyan da ya shigo da cutar kasar." Hukumar ta ce a yanzu mutumin ya na samun kulawa a asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Legas.
A cewar hukumar, sauran mutanen da suka yi mu'amala da mutumin farko a Ogun da Legas za su ci gaba da zama a killace sannan za a yi wa sauran mutanen da ba a yi wa gwaji gwaji ba, har da wadanda suke wasu jihohin.