Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: OPEC ta nemi mambobinta su rage fetur din da suke fitarwa
Kungiyar kasashen da ke da arzikin man fetur, OPEC, ta yi kira ga mambobinta su rage yawan man da suke fitarwa.
OPEC ta yi kiran ne saboda faduwar da farashin man fetur yake yi sakamakon barkewar cutar numfashi ta coronavirus.
Mambobin kungiyar sun gana ranar Alhamis a hedikwatarta da ke birnin Vienna, gabanin ganawar da za su yi da wasu kasashen da ke fitar da man fetur, musamman Rasha.
OPEC tana so a rage ganga miliyan daya da rabi na man fetur din da ake fitarwa a kullum, wanda zai kai kusan kashi uku da rabi na man fetur din da ake fitarwa a halin yanzu.
A ranar Laraba ne, ministar kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa kasar na duba yiwuwar yi wa kasafin kudinta kwaskwarima sakamakon barazanar cutar Coronavirus ke yi wa farashin man fetur a kasuwar duniya.
Ministar ta ce ko da yake har yanzu cutar ba ta shafi yanayin tattara kudin harajin Najeriya da kuma farashin gangar man fetur ba, amma hakan zai iya faruwa idan cutar ta ci gaba da yin tasiri kan tattalin arzikin duniya.