Turkiyya ta bude wa dubban 'yan gudun hijira kofar shiga Turai

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce 'yan gudun hijira 18,000 sun tsallaka zuwa Turai daga iyakokin Turkiyya bayan ya bude masu kofar ficewa.

Ya ce suna tunanin adadinsu zai kai haura 25,000 zuwa 30,000 a kwanaki masu zuwa.

Ya ce Turkiyya ta gaji ba za ta iya ci gaba da hidima da mutanen da ke ci gaba da tserewa rikicin Syria ba.

Girka ta ce ta toshe wa 'yan gudun hijirar kofar shiga kasarta wadanda ta ce na shiga ba bisa ka'ida ba daga Turkiyya.

Jami'an tsaron Girka sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa 'yan gudun hijirar.

Matakin na Turkiyay na zuwa ne bayan harin da dakarun gwamnatin Syria suka kai wa sojojin Turkiyya a arewacin Syria a wannan makon.

Akalla sojin Turkiyya 33 aka kashe a harin Idlib, yanki na karshe da ke hannun 'yan tawayen Syria.

Turkiyya ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya ranar Asabar, inda hare-haren jiragenta marar matuka suka kashe dakarun gwamnatin Syria 26, a cewar kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria da ke Birtaniya.

Syria da Rasha ke mara wa baya, na kokarin kwato garin Idlib daga hannun 'yan tawaye da Turkiya ke marawa baya.

Turkiyya na hidima ne da 'yan gudun hijirar Syria miliyan uku da dubu dari bakwai baya ga na wasu kasashe kamar Afghanistan.

A baya ta Turkiyya ta hana su tsallakawa zuwa Turai karkashin wata yarjejeniya da Tarayyar Turai, amma shugaba Erdogan ya zargi kungiyar da kasa cika alkawalin da ta dauka.

"Watannin da suka gabata mun fada cewa idan aka ci gaba da tafiya haka, za mu bude masu kofa, amma suna ganin wasa ne, kuma bude kofar a jiya," inji shugaba Erdogan.

Ya kuma ce ba zau sake rufe iyakokin ba a kwanaki masu zuwa sai Tarayyar Turai ta cika alkawalinta. "Ba za mu iya hidima da 'yan gudun hijirar ba," inji shi.

Ya ce Tarayyar Turai ta ki bada tallafin da ta yi alkawali a yarjejeniyar 2018 da ta kulla da Turkiya.