Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Amurka ta tabbatar da mutuwar mutum daya
Amurka ta tabbatar da mutum na farko da cutar corona ta kashe a kasar.
Shugaba Trump ya ce wani namiji ne da ya haura shekara 50 cutar ta kashe a jihar Washington da ke arewa maso yammacin Amurka.
Ya ce akwai yiyuwar kara samun wadanda suka mutu, amma Amurka shirye ta ke.
Hukumomin kasar sun ce za ta saka Iran cikin kasashen da aka yi wa Amurka gargadin su kaurace kamar Italiya da Koriya ta kudu.
Sama da mutum 85,000, aka bayar da rahoton suna dauke da cutar a duniya, kuma kusan mutum 3,000 suka mutu, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
China da cutar ta fara bulla ke da yawan wadanda suka kamu da ita kuma a kasar cutar cornavirus ta fi yin kisa.
Me ke faruwa a Amurka?
A lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai ranar Asabar, Shugaba Trumo ya tabbatar da rahotannin da ke cewa mutum daya ya mutu a Washington sakamakon kamura da cutar coronavirus
Jami'an lafiya ba su tantance mutumin ba, amma sun ce ya mutu ne a karamar hukumar King, sun ce bai yi wani balaguro ba zuwa inda cutar ta bulla.
Game da sauran mutum 22 da ke dauke da cutar a yankin, Trump ya ce mutum hudu daga cikinsu "rashin lafiyarsu ta tsananta"
Gwamnan Washington Jay Inslee ya kaddamar da dokar ta baci domin dakile bazuwar cutar a jihar.
Wannan na zuwa bayan bayar da rahoton kara samun wasu mutum uku da suka kamu da cutar coronavirus a jihohin California da Oregon da Washington wanda ke kara haifar da fargaba kan yiyuqar bazuwar cutar tsakanin al'umma.
Akwani wani Ba'amurke da ya mutu a garin Wuhan na China inda cutar ta fara bulla.
Mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya ce dokar hana tafiye-tafiye zuwa Iran yanzu ta shafi duk wani dan kasar waje da ya kai ziyara kasar tsakanin mako biyu.
An kuma bukaci Amurkawa su kauracewa zuwa kasashen Italiya da Koriya ta Kudu.
Mista Pence ya ce Amurka na aiki da jami'ai domin kara tsaurara bincike kan matafiyan da suka shigo Amurka daga kasashen.