An rantsar da shugaban kasa biyu a Guinea-Bissau

Rikici ya kaure bayan an rantsar da shugaban kasa biyu a Guinea-Bissau inda manyan jam'iyyun siyasar kasar ke ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasar.

Tsohuwar jam'iyya mai mulki a kasar ta nada shugaban kasa na rikon kwarya tare da rantsar da sabon firai minista, duk da cewa ta fadi a zaben shugaban kasar na bara.

Ita kuma jam'iyyar PAIGC ta daukaka kara zuwa Kotun Kolin kasar tana neman a ba ta nasarar zaben - amma kotun bata riga ta yanke hukunci ba.

Yanzu kasar na da shugaban kasa biyu da firai minista biyu daga jam'iyyu daban-daban.

Shugaban jam'iyyar adawa, Umaro Sissoco Embalo, wanda ya samu fiye da kashi 50 na kuri'un da aka jefa a zaben na ikirarin cewa shi ne halastaccen shugaban kasar.

A ranar Alhamis ne Mista Embalo ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa a wani otal.

Jam'iyyar PAICG - wadda ta mamaye fagen siyasar Guinea-Bissau tun bayan samun 'yanci kasar a 1974 - ba ta da ko daya daga cikin wadanda aka ba wa shugaban kasar ko firai minista.

Ita ma ta nada shugaban 'yan majalisarta Cipriano Cassamá, a matsayin shugaban kasa. Amma ba shi ne dan takararta a zaben na watan Disamba ba.

Guinea-Bissau na yawan fama da rikice-rikice, inda aka gudanar ko kuma aka yi yunkurin yi juyin mulki har sau tara a kasar daga shekarar 1980.

Masu fasakwaurin miyagun kwayoyi na yawan amfani da kasar a matsayin hanyar jigilar kwayoyinsu daga Kudancin Amurka zuwa kasashen nahiyar Turai.