Ana zuzuta Coronavirus don a sauke Trump – Shugaban Ma'aikatan White House

@

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwararru na aikin hada magungunan rigakafin Coronavirus guda 20 a fadin duniya

Fadar White House ta Amurka ya zargi 'yan jarida da sanya wa mutane fargaba a kan Coronavirus domin ba ta wa Shugaba Donald Trump suna.

Mukaddashin shugaban ma'aikatan White House Mick Mulvaney ya ce: "Mun dauki matakai na musamman a tsawon mako hudu zuwa biyar da suka wuce, amma me ya sa ba su yada ba?

"Me ke faruwa a mako hudu zuwa biyar da suka wuce? Neman tsigewa. Shi kafafen labarai suka fi son magana a kai," kamar yadda ya bayyana a jawabinsa a wurin wani taro ranar Juma'a.

Mick Mulvaney ya ce kafafen yada labarai sun fi ba da muhimmanci ga labarin neman tsige Trump - wanda aka wanke shi daga zargin a watan Fabrairu, saboda tunanin hakan zai karya shugaban.

Ya kara da cewa, "Abin da ya sa suke bayar da muhimmanci a kai yanzu shi ne tunanin da suke yi cewa hakan zai kawo wa Shugaba Trump cikas.''

Don haka ya shawarci kamfanonin duniya da ke nuna damuwa saboda da Coronavirus da su bar sauraron kafafen yada labarai na sa'a 24.

Ana hada rigakafin Coronavirus guda 20 - WHO

Ya zuwa yanzu kwararru na aikin hada magungunan rigakafin Coronavirus guda 20 a fadin duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ana sa ran samun sakamakon gwajin farko da aka yi na magungunan a 'yan makonni masu zuwa.

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da hakan ne yayin jawabin da WHO ta saba yi a kowace rana a kan bakuwar cutar.