Dokar hana bara: Yadda Hisbah ta kama almajirai a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce dokar hana bara da gwamnatin jihar ta kafa ta fara aiki gadan-gadan inda tuni ya zuwa yanzu ta kama yara almajirai 21.
Babban Daraktan hukumar ta Hisbah a jahar, Dr. Aliyu Musa ya bayyana wa BBC cewa an yi sabon tsari a dokar - "yaran da suke makarantu din nan ranar Alhamis da Juma'a su koma makaranta, wannan sabon tsari ne kuma yanzu muka fara aiki a kai."
Ya ce za su ci gaba da kamen yara tare da baza jami'an hukumar a jihar domin tabbatar da cewa kowane yaro ya je makaranta "har da su wadannan makarantu na allo su ma an fada musu bayan yaro ya yi karatunsa na Al Qur'ani, ya yi sauran karatuttukansa ya yi karatun boko."
Ya ce al'umma "ba za ta tafi babu doka ba" - saboda gwamnatin jiha ta sa dokar tilasta wa yara yin karatu kuma duk an yi ne bisa tsarin doka.
A cewarsa, dokar ba wai take hakkin yara bane saboda "babban hakkin yaro shi ne ya yi ilimi, lokacin da ka hana shi ilimi a lokacin ka take masa hakkinsa,"
"Amma wanda ya ce yaro ya zo ya yi karatu ko ya je makaranta toh wannan kare hakkin yaron aka yi."
Dr Aliyu Musa ya ce suna kama almajirai tun baya da aka kafa dokar hana bara a jahar data fara aiki a shekarar 2014, sannan kamen da suka yi yanzu, basu hado da iyayen yaran ba ko malaman nasu ba, amma ya ce nan gaba za su fadada zuwa iyayen wadanda aka kama.







