Coronavirus: Wanne shiri Najeriya ta yi don dakile cutar?

Lokacin karatu: Minti 2

Samun mutumin da ya kamu da cutar numfashi ta coronavirus karon farko a Najeriya ya sa 'yan kasar na tambaya: wanne shiri hukumomi suka yi na dakile ta?

Ranar Alhamis ne Hukumomin Lafiya a Najeriya suka tabbatar da bullar coronavirus wadda ake kira Covid-19 a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin kasar.

A sanarwar da ya fitar, Ministan Lafiya na Najeriya, Dr Osagie Ehanire, ya ce wani dan kasar Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo Lagos daga birnin Milan.

"Sakamakon gwaji da aka gudanar a asibitin Koyarwa na Jami'ar Lagos ya tabbatar da mutumin yana dauke da cutar.

"Ana duba lafiyarsa a Asibitin Kula da Cututtuka Masu Yaduwa a Yaba, kuma marar lafiyar bai nuna alamomi masu muni ba," in ji shi.

Wannan shi ne karon farko da aka samu bullar cutar a nahiyar Afirka kudu da hamada.

Hanyoyi 4 na kare kai daga coronavirus

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Minista Ehanire ya ce gwamnatin kasar ta hannun Ma'aikatar Lafiya ta kara tsaurara matakai don dakile cutar nan take.

Ya ce sun zage damtse wurin ganin Cibiyoyin Kula da Lafiyar Gaggawa a fadin kasar sun tashi tsaye domin gudanar da ayyukansu, yana mai cewa za su hada gwiwa da cibiyar da ke Lagos don shawo kan cutar.

"Muna so mu tabbatar wa 'yan Najeriya cewa cibiyoyinmu na ko-ta-kwana sun kara kaimi wurin gudanar da ayyukansu tun da aka samu labarin bullar cutar a China, kuma za mu yi amfani da dukkan matakan da gwamnati za ta iya dauka domin dakile ta", a cewar ministan.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya su kula da lafiyarsu, musamman tsaftar hannaye da hanci da sauran sassan jiki da ke taimakawa wurin yin numfashi.

Ya bukaci duk mutumin da ya ji alamar rashin lafiya, irin su zazzabi da mura da tari, ya kira wannan lamba: 0800 970 0000-0010.