Ana takaddama tsakanin Baban Chinedu da hukumar fina-finai ta Kano kan marigayi Ibro

Wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da kuma jarumin fina-finan Kannywood, Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu.

Takaddamar ta samo asali ne bayan da aka aike wa Baban Chinedu wata takarda a kan wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram yana zargin cewa gwamnatin Kano ta bai wa shugaban hukumar tace fina-finan N5m domin mika su ga iyalan marigayi Rabilu Musa Ibro.

Baban Chinedu dai makusancin Ibro ne, kuma ya ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta bai wa Isma'il Na'abba Afakallah kudin ne a matsayin gudunmuwar bikin 'yar gidan marigayi Ibro kusan shekaru biyu da suka wuce.

Lauyoyin Malam Afakalla ne suka aike wa Baban Chinedu takardar inda suka nemi ya janye kalaman da ya yi a bidiyon ko kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Lauyan Afakallah, Barista Abdullahi Musa Karaye, ya shaida wa BBC cewa duk abin da Baban Chinedu ya fada a cikin bidiyon ba gaskiya ba ne.

Ya kara da cewa ya wallafa bidiyon ne da zummar bata sunan shugaban hukumar tace fina-finan.

Amma Baban Chinedu ya shaida wa BBC cewa "Ba zan janye kalaman da na yi ba, kuma ina da hujjojin da na dogara da su kan zargin da nake yi wa Afakallahu ya karbi kudi."

Baban Chinedu ya ce "Bashi aka sa iyalan Ibro suka karbo na kayan dakin da suka kai N700,000 ga shi tsawon shekara biyu shiru ba wani bayani, sai daga baya ne iyalan marigayin suka sayar da wani gidan gado sannan suka biya masu kayan kudin."

Ya kara da cewa: "Ko da na yi wa Afakallah tuni kan batun kudin, sai ya ce takardar amincewar gwamna a biya kudin na dab da fitowa, amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu."

Afakallah ya ba wa Baban Chinedu awa ashirin da hudu da ya janye kalaman nasa, sannan ya bayar da hakuri idan bai yi haka ba zai gurfanar da shi a gaban kuliya.