BBC Hausa: Hanya biyar mafiya sauki na sauraron shirye-shiryen rediyo

Aishatu Musa
Bayanan hoto, Aishatu Musa ke nan a bakin aiki a watan Maris na shekarar 2013
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja Bureau

Idan irina ne kai wanda ba ya iya barin sauraron labaran BBC saboda wani aiki kamar wanki ko kallon kwallo, ko kuma ba ka son yawo da rediyo a hannu don kar abokanka su ce maka bakauye, to ga mafita.

Kai ko ma ba irina ba ne kai, ai ba za ka so a ce ba ka san halin da duniya ke ciki ba kawai don rediyonka babu batir ko ya lalace.

Babu yadda muka iya, duk lokacin da aka ambaci BBC Hausa rediyo ne ke fara zuwa a tunanin mutane.

Ko ma dai mene ne, akasarin miliyoyin masu sauraronmu na kama mu ne ta akawatiin rediyo, babba ko karami.

Saboda haka har yanzu BBC na alfahari da akwatin rediyo da masu rike shi a hannu ko a kafada ko kuma a karkashin bishiya yayin iskar bazara.

Amma ga wasu hanya biyar mafiya sauki da za ku iya sauraron Sashen Hausa na BBC.

1. Manhajar BBC Hausa

Bajon BBC Hausa
Bayanan hoto, Shekara sama da 60 muna kawo muku halin da duniya ke ciki

Wannan manhaja ce da za ku sauke a kan wayoyinku daga ofishin manhajoji kamar Play Store ko kuma App Store ga masu amfani da iPhone.

Sai dai BBC ba ta yada shiri kai-taye ta wannan manhaja, sai an gama sannan za ku saurare shi.

Amma fa da zarar an gama da 'yan mintuna kawai data za ku kunna ku shiga ku zabi shirin, in kuka ga dama ma sai a makala hedifom a kunne - ba sai an damu wani a gefe ba ke nan.

Sauraro a wannan manhaja kyauta ne, in ban da data da za ku saya kawai.

2. Manhajar Simple Radio

Dakin shirye-shiryen BBC na Legas
Bayanan hoto, Akwai sashen Pidgin da Yoruba da Igbo na BBC da ke yada shirye-shiryensu daga Legas

Kamar waccan, ita ma wannan saukewa za ku yi a wayarku domin jin Ahmad Abba Abdullahi ko Sulaiman Ibrahim ko Badariyya Tijjani Kalarawi da sauran ma'aikatan BBC.

Shi kuma Simple Radio ana iya sauraro kai-tsaye ne kawai. Idan aka kammala shiri to shi ne zai yi ta maimaita kansa har sai an yi sabo.

Akwai daruruwan gidajen rediyo a kan wannan manhaja, ciki har da sauran sashe-sashe na BBC kamar Ingilishi da Arabiyya da Indiyanci (Hindu) da dai sauransu.

Amfani da wannan manhaja kyauta ne kuma dole ne data ta kasance a kunne a lokacin da kuke sauraro.

Da zarar an kammala Shirin Hantsi ba za ku sake sauraronsa a Simple Radio ba saboda Shirin Safe kawai zai rika maimaitawa.

3. Manhajar Hausa Radio

Lasifikokin yada labarai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Muna yada labarai daga Abujan Najeriya da kuma birnin Landan

Manhajar Hausa Radio ta bambanta da saura, saboda kuna iya sauraron shiri kai-tsaye sannan kuma kuna iya sauraro bayan an kammala, har ma ku yi tariyar gaba ko baya.

Kuna iya sauraro data dinku a kashe. Da zarar an gama karanto labaran duniya za ku iya kashe data har a gama shirin ba tare da layi ya katse ba.

Kawai Play Store za ku shiga ku bincika sunan 'Hausa Radio', sai ku sauke a kan wayarku.

Kyauta ne amfani da wannnan manhajar kuma ita ma ta kunshi gidajen rediyo da yawa masu amfani da Hausa kamar BBC, da ma sauran gidajen rediyon FM a Najeriya.

Akwai Shirin Ra'ayi Riga a ciki da za ku yi ta saurara na tsawon mako har sai gabatar da sabo.

4. Manhajar TuneIn

Ma'aikatan BBC
Bayanan hoto, A wannan hoto akwai Elhadji Diori Coulibaly da Isa Sanusi da Aminu Abdulkadir a bakin aiki a watan Yulin 2012

Kamar waccan, ita ma wannan saukewa za ku yi a waya, kawai a shiga sauraron halin da duniya ke ciki.

A wannan manhaja ana iya sauraro kai-tsaye kuma da zarar an kammala shiri to shi ne zai yi ta maimaita kansa har sai an yi wani sabo.

Ana iya sauraro kyauta a TuneIn amma a wasu wuraren bayan mako guda ko kuma wata daya sai an biya kudi.

5. bbchausa.com

Shafin bbchausa.com

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Ga sashen shirye-shiryenmu nan a shafin bbchausa.com

Idan duk kuna ganin sauke manhajojin nan za su yi muku wuya, sai ku garzaya shafinmu na bbchausa.com, ku duba gurbin shirye-shiryenmu domin sauraronsu a duk lokacin da kuke so.

Kowanne shiri yana da gurbinsa tun daga na safe har zuwa na dare da kuma ra'ayi riga da za ku yi mako guda kuna sauraro har sai an gabatar da sabo.

Kuna iya sauraro kai-tsaye ko kuma idan an gintse shirin amma dole ne data ta kasance a kunne har zuwa karshensa.