Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ya kamata a fara koyar da illar shan kwaya a jami'a a Najeriya'
Shugaban asibitocin kula da masu lalurar kwakwalwa na gwamnatin tarayya a Najeriya ya bukaci a sanya darussan illar shan miyagun kwayoyi wato drug abuse manhajar karatun jami'o'in kasar.
Dakta Shehu Saleh ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar a koya wa dalibai ilimin yaki da shan miyagun kwayoyi kamar yadda ake koyar da sauran fannoni na kiwon lafiya a jami'a.
Ta'ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasan Najeriya babbar matsala ce da mahukunta ke cewa suna yaki da ita a ko da yaushe.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na watan Yunin 2019 ya ce kusan mutum miliyan 35 ne a duniya ke fama da matsalar miyagun kwayoyi, fiye da yadda aka yi tsammani tun da farko.
"Kamar yadda ake yin darussan Biology da Physics da Chemistry ya zama shi ma darasi ne na musamman da mutum zai nema kuma a ba shi horo," Dakta Shehu ya bayyana.
Dakta ya ce an gayyace shi ne wani taron lacca a jami'ar birnin Kebbi, inda ya lura cewa jami'o'in Najeriya ba su da irin wannan tsarin.
"Muna bukatar kwararru da yawa. Kamar yadda ake yaye dalibai su je su yi aikin likita haka ya kamata a samu masu aiki a bangaren miyagun kwayoyi.
"Akwai wani darasi da ake kira General Studies wato wanda kowane dalibin yake yi, ya kamata a saka maganar shan kwaya a cikinsa saboda a san illolinta."
Wani bincike da BBC ta yi a 2018 ya kai ga rufe wasu manyan kamfanonin sarrafa magunguna tare da haramta sayar da maganin tari mai sinadaran Kodin da Tramadol a kasar.
Tsohon kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, CP Muhammad Wakili wanda ake yi wa lakabi da Singham, ya yi suna wurin yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi.
A wata hira da BBC a watan Yunin 2019, CP Singham ya bayyana yadda ya fara yaki da shan kwaya da kuma nasarorin da ya samu.