An daure wata mata da ta bude kofar jirgi a sararin samaniya

Chloe Haines

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Chloe Haines ta daki wata ma'aikaciyar jirgin lokacin da ta yi kokarin hana ta bude kofar jirgin a sararin samaniya

An yanke wa wata mata hukuncin shekara biyu a gidan yari, sakamakon bude kofar jirgin sama ana tsaka da tafiya, abin da ya janyo wasu jiragen yaki guda biyu suka kai masu agajin gaggawa.

Chloe Haines, mai shekara 26 mazauniyar High Wycombe, ta yakushi daya daga cikin ma'aikatan jirgin yayin da take ihun cewa "sai na kashe ku dukanku, kamar yadda aka shaida wa kotu.

Jiragen yaki biyu samfurin RAF sun zabura domin yi wa jirgin rakiya zuwa filin jirgin sama na Stansted.

Haines, wadda ta amsa laifi biyu, an yanke mata hukunci ne a Kotun Chelmsford Crown.

Ta amsa laifin saka rayuwar fasinjoji cikin hadari da kuma cin zarafi ta hanyar duka.

Lamarin ya faru ne a jirgin Jet2 da ke dauke da fasinja 206 a kan hanyarsa ta zuwa Dalaman na kasar Turkiyya a ranar 22 ga watan Yunin 2019.

Haines ta ce "ta sume kuma ba za ta iya tuna abin da ya faru ba" bayan ta sha magani tare da barasa, kamar yadda mai shigar da kara Michael Crimp ya fada wa kotu.

Ma'aikaciyar jirgin, Charley Coombe, ta sha duka da yakushi yayin da ta yi kokarin hana Haines bude kofar jirgin.

Wani fasinja ya fada wa kotun cewa "lallai ya yi fargabar za ta iya bude kofar".

Mai shigar da kara ya fada wa kotu cewa Haines ta yi kururuwar "ina so na mutu" kuma "sai na hallaka ku baki dayanku".

Lauyan Haines, Oliver Saxby QC ya bayyana ta a matsayin "mai neman husuma tare da tarihin manyan abubuwa da ta aikata a baya".