Wasu kyawawan hotuna da matasa suka nuna yadda rayuwarsu take

Masu daukar hoto 'yan shekara tsakanin shekara 16 zuwa 19 sun yi sharhia hotuna kan yanayin zamantakewarsu a bangaren siyasa da kuma sauyin yanayi a Birtaniya.

Hoton wata matashiya

Asalin hoton, Benedicte Lungwa-Loussi

Wani wajen daukar hoto da ke Shoreditch, a gabashin birnin Landan na daukar hotuna daban-daban.

Masu daukar hoto a wajen 'yan makaranta wadanda kuma ke aiki tare da kungiyar zane-zane da kuma wata jami'ar koyon fasahar kere-kere a Landan su kan baza hotunansu a wajen baje kolin hotuna.

Ga wasu daga cikin hotunan da masu daukar hoton suka dauka da ma bayanansu.

Wata matashiya 'yar Birtaniya mai daukar hoto Fatimah Al-Zahraa Zahmoul

Hoton wata mata ta sanya kayan da ya nuna al'adu uku a jikinta ta na kallon kamara

Asalin hoton, Fatimah Al-Zahraa Zahmoul

"Ni jerin hotunana na nuna yanayin al'aduna. Na yi kokari na sanya kayan da ya nuna al'adu uku a tare da ni".

"Na mayar da hankali a kan tallata kabilun da na fito daga cikinsu, wato Aljeriya da Punjabi na Indiya.

" A matsayina ta 'yar Birtaniya mazauniyar Landan, ina kokari na ga na fito da al'aduna a ko da yaushe.

" Ziyarar da na kai Aljeriya shekaru da suka gabata, ta taimaka mini na gano wani bangare na asalina.

" Na kan bayyana wani bangare na al'aduna na Indiya, kamar wajen sanya kayan kawa da makamanyansu".

Presentational grey line

Hotunan Filip Skiba

Hoton wani matashi ya na zaune a dandamalin kasa yana kallon kamara

Asalin hoton, Filip Skiba

"Aikin da nake yi a yanzu na The Fluid State, ya na sa mutane su fahimci yadda mutane ke zabar jinsin da za su kasance da yadda hakan zai yi tasiri a kansu.

"Na samu kwarin gwiwa ne daga raye-rayen zamani, ina matukar son yadda masu rawa ke yi da jikinsu suna rawa.

"Na yi amfani da wannan kwarin gwiwar ina gabatar da hotunana".

Presentational grey line

Hoton wasu matasa daga Leigha Cohen

Hoton Leigha Cohen

Asalin hoton, Leigha Cohen

"Ina son hotunana su rinka nuna yadda matasa suke kamar a yanayi na tausayi".

"Na tattauna da mata da maza 'yan tsakanin shekaru 16 zuwa 18. Na son kowanne daga cikinsu, na kuma yi musu tambaya a kan ko su waye su da kuma yadda suke a gidajensu".

Presentational grey line

Hotunan Genesis Tennison

Hoton wata mata ta sanya riga wadda za a iya ganin duk wani motsinta

Asalin hoton, Genesis Tennison

"Ina da sha'awar kirkirar hotunan da za su rinka magance kalubalen da al'umma ke fuskanta a ciki da waje".

"Duk wani da zan dauka yana da manufarsa".

Presentational grey line

Hotunan Benedicte Lungwa-Loussi

Hoton wasu yammata sun rikewa juna kai

Asalin hoton, Benedicte Lungwa-Loussi

"Kalar jikinmu ita ke nuna alamar ko mu su waye kuma ba za a iya sauya mu ba, kuma muna alfahari da kalar jikinmu.

"A matsayinmu na bakaken fata, dole mu yi alfahari da kalar jikinmu da ma yadda muke.

"Ina son mutane su rinka alfahari da kansu su kuma nuna jin dadin da kalar jikinsu".

Presentational grey line

Hotunan T'Shan Barnes

Hoton wata mata kwance tana sauraron kida a headphones

Asalin hoton, T'Shan Barnes

"Wannan hoton wani bangare ne na irin rayuwar da nake so a rayuwata. Ina so na rinka jin kida daga kwance ta hanyar amfani da abin sauraro wato headphone.

"Na dauka a wani wajen daukar hoto inda aka sanya furanni a bayan inda aka dauki hoton".