AU: Guterres ya yi Alla-wadai da yakin Libya

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da rikicin da ke ci gaba a kasar Libya, yayin da aka shiga wuni na biyu na taron kolin Tarayyar Afirka.

Ya ce katsalandan din kasashen waje a kasar da cewa wani babban abin kunya ne. 

Ya ce ci gaba da rikicin ya ba shi kunya, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma takunkumin hana bazuwar makamai da aka cimma a watan jiya.

"Akwai takunkumin makamai amma ana keta ta gatse-gatse," in ji Mista Guterres.

Mista Guterres ya soki lamirin kasashen duniya saboda mara baya wa bangarorin da ke yaki a Libya baya.

Ya kuma ce yakin 'yan barandan kasashe ya taimaka wajen bazuwar rikicin 'yan ta-da-kayar-baya a Sahel.

"Na fahimci fushin da kasashen Afirka suke yi dangane da wannan yaki da ake yi tun shekarar 2011. Zuwa yanzu an gane cewa akwai kasashen da ke samar da makamai a wannan rikici," a cewarsa.

Babban Sakataren ya bukaci Afirka ta jagoranci shirin wanzar da zaman lafiya bayan korafin da shugabanin nahiyar suka kai masa na cewa an mayar da su gefe a kokarin kawo karshen rikici.

Afirka za ta iya jagorantar shirin samar da zaman lafiyar?

Mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya, Kabiru Adamu ya ce dole kasashen Afirka su dauki shirin da muhimmanci idan da gaske suke.

Ya ce akwai asusun African Union Peace Fund wanda kasashen Afirka, suka tara kudi dala miliyan 124 wanda za a iya amfani da shi wurin tura dakaru Libya.

Sannan ya ce dole sai idan Libya ta ba da hadin kai kafin a iya cimma wannan buri na samar da zaman lafiya.

"Wannan shi ne muhimmin abu na farko da ya kamata a samu kafin a iya yin koma," in ji Kabiru Adamu.

Ya ce kuma ya kamata shugabannin kasashen nan su gaya wa kansu gaskiya, su mayar da hankali su dauki matakai kwarara wadanda za su taimaka wa halin da ake ciki.

Rikicin ya fara ne lokacin wani juyin juya hali da kasashen Larabawa suka yi a 2011.

Dakarun da ke samun goyon bayan kungiyar Nato sun hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekarar, wanda tarihi ya nuna cewa shi ne ya fi dadewa kan karaga duk da fatan da ake samu a lokacin daga 'yan Libya da kuma kasashen duniya.

Tun lokacin, kasar take fuskantar yakin basasa.

Bayan shafe shekaru ana yaki, Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka wajen kafa gwamnati karkashin Firai Minista Serraj. Gwamnatinsa karkashin jam'iyyar GNA da ke babban birnin Tripoli don hada kan kasar.

Ba kowa ne ya goyi bayan yarjejeniyar ba kuma Janar Haftar na son mulkar kasar.

Ya kafa dakarunsa LNA a gabashin kasar da ke da mazauni a biranen Tobruk da Benghazi. Ya yi ikirarin cewa shi kadai ne zai iya maido da tsaro tare da yakar rikicin masu da'awar kishin addinin Musulunci.

Dakarun Janar Haftar sun bazu zuwa birnin Tripoli tun Afrilun 2019. A wannan watan, sun yi yunkurin kwace iko da wani muhimmin birni mai suna Sirte.

Amma masu ta da kayar baya suma sun kafa sansaninsu a birane daban-daban, sannan wani reshen kungiyar IS su ma suka bullo inda suke gudanar da harkokinsu a cikin dazuka.

Me ya sa aka damu da batun?

Da alama akwai kasashe da dama da ke da hannu a rikicin na Libya kuma ga dalilin da ya sa suka damu.

  • Libya ce kasar da ta fi ma'ajiyar mai mafi girma a nahiyar Afirka sannan babbar mai samar da iskar gas ce
  • Libya kuma hanya ce ga bakin haure ta isa Turai
  • Sannan yadda IS da sauran kungiyoyin ta'addanci suka kafu abin tsoro ne ba wai ga kasashe makwabta ba
  • In dai yakin Libya ya ci gaba, rikici na iya bazuwa zuwa wasu kasashen.