Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ofishin 'yan sanda masu kwance bam ya yi bindiga a Ekiti
Ofishin 'yan sanda masu kwance abubuwa masu fashewa ya yi bindiga a safiyar ranar Asabar a garin Ado Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Da take tabbatar da tashin ababen fashewan a shafinta na Twitter, gwamnatin jihar ta ce lamarin ya lalata sassan ofishin 'yan sandan da wasu gine-gine da ke makwabtaka da shi.
Sanarwar da kwamishinan yada labaran jihar Ekiti Aare Muyiwa Olumilua ya fitar ta kara da cewa ba a samu asarar rai ba.
Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ziyarci inda ababen fashen suka tashi tare da kwamishinan 'yan sandan jihar da kuma shugaban majalisar sarakunan jihar.
Hukumomin jihar basu yi karin bayani game da musabbabin tashin ababen fashewan ba, amma sun bukaci jama'a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu domin an riga an shawo kan matsalar.