Aisha ta tuna da mahaifiyarta Maryam Babangida

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Diyar tsohon shugaban Najeriya Aisha Babangida, ta ce ta gayyaci dukkanin matan tsofaffin shugabannin kasar domin a koyi wani abu daga tarihinsu da ayyukan da suka yi a baya na taimaka wa kasa.

Aisha ta bayyana hakan ne a wata hira da BBC ta yi da ita a bayan taron, wanda ta shirya shi don tunawa da shekara 10 na mutuwar mahaifiyarta Maryam Babangida.

Ta kuma bayyana cewa ya kamata a fara tallafa wa mutane musamman na kusa, ta hanyar ba su abubuwan da zai inganta rayuwarsu.

Bidiyo: Abdulbaki Jari