An kashe 'yan sa kai shida a Birnin Gwari da mutum bakwai a Tsafe

Rahotanni daga Najeriya na cewar barayin shanu sun kashe kimanin mutane 13 tare da kora shanun da ba a san yawansu a wasu kauyukka da ke jihohin Kaduna da Neja da kuma Zamfara.
Shida daga cikin mutanen 'yan sintiri daga Birnin Gwari suka mutu a yayin taho mu gama da barayin, wasu kuma suka sami raunuka a cikinsu.
Yayin da Tsafen jihar Zamfara kuma, barayin suka kashe mutum bakwai bayan kora dukkan dabbobin garin.
An kashe 'yan sa kan ne da yammacin ranar Litinin a wani ba-ta-kashi da 'yan sa kan suka yi da 'yan bindigar.
Wani jami'i a karamar hukumar Birnin Gwari da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa da BBC cewa an yi jana'izar mutum shida daga cikin 'yan sa kan.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun sato shanu da dama ne shi ne 'yan sa kan wadanda suka fito daga Birnin Gwari da kuma wasu yankunan jihar Neja suka far musu.
A nan ne aka yi ba-ta-kashi, sai 'yan bindigar suka samu galaba a kan 'yan sa kan, saboda sun yi musu kawanya.
Jami'in ya ce, baya ga wadanda suka rasa ran nasu, akwai wasu daga cikin 'yan sa kan da suka samu raunuka wadanda yanzu haka suke kwance a babban asibitin Birnin Gwari suna karbar magani.
Akwai kuma wadanda har yanzu ba a gansu ba daga cikin 'yan sa kan.

Dubban mutane ne ke tserewa daga kauyuka daban-daban na yankunan kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari inda suke neman mafaka a garin Buruku na jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Yankin dai na Birnin Gwari ya jima yana fama da rikice-rikice musamman na barayin shanu da 'yan bindiga dadi da kuma masu garkuwa da mutane.
A hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu a 'yan kwanakin nan, al'amarin ya yi sandin asarar rayuka da raunata mutane da dama, baya ga awon gaba da ake zargin maharan sun yi da mutane da kayayyaki.












