Za a bai wa fararen hula makamai don yaki da 'yan ta'adda a Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a Burkina Faso na fama da karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi wanda ke addabar yankin, lamarin da yasa suke shirin fara bai wa fararen hula makamai.
Gwamnatin kasar na fuskantar matsin lamba a kan ta dauki sabbin matakai na kawar da 'yan ta'adda.
A watan Janairun 2020 kadai, an kashe mutum a kalla 60 a wasu hare-hare hudu da aka kai a karo daban-daban a arewacin kasar.
A kwanan nan 'yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri'ar amincewa da taimaka wa fararen hula a wani yunkuri da suke ganin zai taimaka wajen yaki da masu tayar da kayar baya.
Hare-haren masu tayar da kayar bayan wadanda ke da alaka da kungiyar al-Qaeda da IS, sun karu a shekarar da ta wuce, lamarin da ya tursasawa mutane fiye da rabin miliyan barin gidajensu.
Masu suka na tantama a kan cewa ko sabbin matakan za su taimakawa mutane, amma kuma gwamnati ta ce akwai bukatar taimakon 'yan sa kai domin yaki da 'yan ta'addar.
Sabuwa dokar da 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da ita ta ce sojojin kasar ba su da yawa ba su da kayan aiki da kuma horon da za su iya yakar masu tayar da kayar bayan.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai damuwa a kan sabbin matakan da za a dauka inda ake ganin zai iya haddasa rikicin kabilanci tare da iza zaman dar-dar din da ake fama da shi a tsakanin manoma da mafarauta.
Akwai dai zargin da ake cewa su ma kan su jami'an tsaron kasar na cin zarafin 'yan kasar lamarin da a ko da yaushe gwamnatin kasar ke musantawa.
Za dai a dauki duk wani dan kasar da ya kai shekara 18 aikin sa kan idan har ya na da sha'awa.

Asalin hoton, Getty Images
Za dai a dauki wadanda za a bai wa makaman aiki ne tun daga matakin kananan hukumomi inda shugabannin kananan hukumomin za su duba yadda ake daukar aikin tare da horar da yaran.
A Burkina Faso, ba kamar a Mali da Najeriya ba, inda fararen hula ke samarwa kansu makamai suna kare kansu da kuma dukiyoyinsu daga masu tayar da kayar baya, su a can sai gwamnati ta san da mutum, kuma ita za ta ba su makaman da za su kare kan nasu.
Za a dauki fararen hular da za a bai wa makaman ne aiki a hukumance daga kuma bangarorin kabilun daban-daban.
Abin fargabar a nan shi ne, mafi yawancin bangarorin kasar na karkashin ikon 'yan ta'adda, don haka akwai fargabar yadda za a bai wa 'yan bangaren makaman da za su kare kansu.
Yawancin bangaren arewaci da kuma bangaren arewa maso gabashin kasar da ke iyaka da Mali da Nijar, sun fi fuskantar hare-hare.
Ko waddane irin horo za a bai wa masu aikin sa kan?
Ba a sanar da lokacin da za a dauki fararen hular wannan aiki na sa kai ba.
A cikin dokar, an ce za a dauki mutane a kalla 10 daga kowanne kauye.
Idan har kuma aka dauke su, za a ba su horo na mako biyu, kamar yadda za su rike makamai da yadda za su yi amfani da makaman.
Ba a san wanda zai ba da wannan horo ba ya zuwa yanzu.

Bayan an dauke su aiki, za a ba su makamai tare da abubuwan da za su rinka magana a tsakaninsu da sauran jami'an tsaro, amma kuma ba su da inifom.
Yayin da masu aikin sa kan za su sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar aiki na tsawon shekara guda ba tare da biyan ko sisi ba, za a rinka ba su dan alawus kuma za su rinka samun tallafi.
Za a rinka biya musu kudin magani idan sun ji rauni tare da biyansu diyya idan har aka ji musu raunin da zai ja musu nakasa.
Za kuma a rinka daukar nauyin jana'izar su idan sun mutu a lokacin aiki.
Me ake so masu aikin sa kan su rinka yi?
Ana so masu aikin sa kan su kasance suna nan a ko da yaushe a kauyukansu.
Ana kuma so su rinka taimaka wa ayyukan sojoji da 'yan sanda wajen kare kauyukansu.












