Annobar Coronavirus ta yi kisan farko a wajen China

Asalin hoton, EPA
Coronovirus ta yi kisan farko a daya cikin kasashen da aka samu bullar annobar bayan kasar China inda cutar ta samo asali.
Mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar a wajen China ya rasu ne a kasar Filifins.
Hukumar lafiya ta duninya WHO ta ce da alama mutumin mai shekara 44 ya kamu da cutar ne kafin zuwansa Filifins.
Mutumin ya isa Filifins ne daga Hong Kong bayan ya baro yankin Wuhan tare da wata mata da a makon da ya gabata aka gano cewa tana dauke da cutar.
An fara kwantar da mutumin ne a asibiti a birnin Manila inda daga bisani rashin lafiyarsa ta tsananta.
WHO ta ce zuwa yanzu annobar ta kashe mutum fiye da 300, galibinsu a yanin Hubei, yayin da wasu fiye da 14,000 suka maku da cutar.
Kasashen Amurka da Australia da New Zealand da Rasha da Japan da Pakistan da Italy da Indonisia da Singapore da Koriya ta Kudu sun dakatar da shigowar baki daga China.
Amurka na killace 'yan kasarta da suka dawo daga yankin Hubei na kasar China na tsawon kwana 14. Wadanda suka dawo daga wasu sassan kuma za a bar su su rika lura da yanayin lafiyarsu.
Yawan wadanda suka kamu a barkewar annobar coronavirus ya haura na wadanda suka kamu da kwayar cutar Sars a shekarar 2003, inda mutum kimanin 30 suka kamu da annobar.











