Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasika daga Afirka: Rundunar Amotekun da matsalar satar mutane
Cikin jerin wasikun da muke samu daga jaridun Afirka, tsohon babban editan jaridar Daily Trust, Mannir Dan Ali ya mayar da hankali kan takaddamar da ake shirin yi don magance matsalar tsaro a kasarsa.
A makon da ya gabata, na taimaka wajen biyan kudin fansar mace da yaran wani abokina su biyu. Suna hannun masu garkuwar har tsawon kwana takwas bayan da aka dauke su daga gidansu a arewacin Kaduna.
Abun da na yi, ba wani sabon abu ba ne, ire-iren labaran da aka saba ji ne kan matsalar tsaro da ake fama da ita a fadin kasar.
Ana ta sukar gwamnatin tarayya kan rashin samar da isasshen tsaro a kasar, hakan ne ya sa gwamnonin jihohi shida na kudu-maso-yammacin Najeriya suka samo wa kansu mafita.
Sun sanar da cewa suna shirin samar da nasu rundunar tsaron da za a kira da 'Amotekun' da kalmar Yoruba, wadda ke nufin 'Argini' wato wani nau'i na damisa.
Har yanzu dai ba a san takamaiman aikin da za su yi ba yayin da jihohin ke ci gaba da kammala shirye-shiryensu, sai dai a shirye take ta dauki sabbin ma'aikatan tsaro tare da ba su ikon kama masu laifi.
Zargin shirya 'yar a-ware
Shirin ya hassala hukumomin kasar ya kuma sa wasu zargin jihohin guda shida na shirin ballewa daga Najeriya, kasar da ke da yawan al'umma miliyan 200 da kuma yaruka daban-daban. Yarabawa na daya daga cikin manyan yaruka uku na kasar.
A makon da ya gabata, gwamnonin sun gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo domin rage zarge-zarge da ake yi musu.
Sai dai idan akwai mai tsammanin cewa bayan ganawar tasu hakan zai kawo karshen takaddamar, to lallai zai ji kunya.
Bayan kammala ganawar tasu, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu wanda ya jagoranci gwamnonin shida, ya ce sun cimma yarjejeniya.
Ya ce, jihohin za su samar da dokokin kafa Amotekun su kuma tafiyar da shi dai-dai da tsarin 'yan sandan kasar.
Sai dai nan take, wata kungiyar al'adun gargajiya ta Yarabawa, 'Afenifere' wadda ke mara wa sabon shirin baya, ba tare da wata-wata ba sun soke yarjejeniyar inda suka ce, gwamnatin tarayya ba za ta fada wa yankin kudu-maso-yamma yadda zai bai wa mutanensu kariya ba.
Haka kuma an samu ire-iren wadannan maganganun kan sauran al'amura, wanda ya bai wa masu adawa damar ganin cewa gwamnatin tarayya ta samu hujja mai karfi kan lamarin.
Kafafen yada labarai da ma na sada zumunta na ta yada labarai da kuma ra'ayoyin mutane a kan batun.
Shafin jaridu da dama na dauke da labarin Amotekun yayin da gidajen talabijin da rediyo ke tattaunawa kan batun a shirye-shiryensu da kuma labarai.
Haka kuma kafafen sada zumunta, na ta tattaunawa kan batun tun farkon samar da shirin makonnin da suka wuce.
Kuna iya son karanta wadannan:
'Yan siyasa da dama ba su da kudin da zai sa su kaucewa wannan shirin na 'damisa'. Sai dai an samu daya daga cikin manyan 'yan siyasa da ya kokarta ya fadi albarkacin bakinsa kan batun.
Bola Tinubu, sanannen dan siyasa daga kudu-maso-yamma, wanda ya mara wa Muhammadu Buhari baya sosai a zaben 2015, ya fadi albarkacin bakinsa kan lamarin.
A yayin da Bola Tinubu ke sa ran samun goyon bayan Shugaba Buhari kan tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, sa'annan kuma yana taka tsantsan wajen gurbata alakarsa da mutanensa na kudu-maso-yamma, ana ganin bangarorin biyu sun sami goyon bayan Tinubu kan lamarin.
Wasu ra'ayoyin mutane kan lamarin ya nuna rashin yarda tsakanin yankunan biyu na Najeriya.
A lokacin da tsohon dan siyasar arewa, Balarabe Musa ya bayyana nasa ra'ayin kan Amotekun, ya ce, wannan shi ne 'somin tabin' rarrabuwar kan jamhuriyyar Yarabawa.
Ba a bata lokaci ba, ya samu martani masu zafi.
Fitattaccen marubucin nan wanda ya karbi lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya ce "dawo da rarrabuwar kawuna tsakaninmu ba hanyar bullewa ba ce, musamman a wannan lokaci da ake ganin gazawar gwamnati."
Marubucin wakoki da kuma wasan kwaikwayo ya kara da cewa, "masu rura wutar kafa Amotekun sun nanata cewa su dai 'yan a bi yarima ne kawai a sha kida".
Sai dai, Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya ce, jami'an tsaro da ake shirin kafawa sun saba wa dokokin kasa, tun da har kundin tsarin mulki ya bayar da irin wannan karfin ikon ga gwamnatin tarayya.
Malami ya ayyana cewa: "Amotekun ba ya cikin tsarin mulki kuma ba a samar da shi ta hanyar da ta dace ba".
Yayin da shugabanninmu ke ta muhawara kan lamarin kundin tsarin mulki, 'yan Najeriya marasa galihu wadanda ba na kudu-maso-yamma kawai ba a fadin kasar baki daya, na cikin fargabar masu garkuwa da mutane da 'yan ta'adda sannan a arewa-maso-gabas kuma ana fama da matsalar 'yan Boko Haram.
Suna kisa da yanka mutane da kuma sanya mutane cikin talauci ta hanyar hana su gudanar da kasuwancinsu cikin zaman lafiya.
Bayan wadanda suka kware a satar mai daga bututu, akwai kuma 'yan ta'addan da suka mamaye garuruwa da kauyuka, suna hana mutane da dama noma da kiwo.
Wannan ya hada da makiyaya da ke kashe manoma.
Martanin 'yan sintiri
Sai dai matakan da aka dauka ga dukkan alamu 'tsoka daya ce a miya ', sannan kuma ake bayar da shawarar daukar wani matakin na daban - ta tsararriyar hanyar da ta dace, kafin mutane su fara daukar mataki ko shiga aikin sa-kai da kansu.
A makonnin da suka gabata ne kuma, a wani yanayi da ke nuna mutane na zartar da hukunci da kansu ba tare da hukuma ba, an samu rahoton cewa gungun mutane a jihohin Bayelsa da Akwa Ibom sun kona wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne kurmus har lahira.
A babban birnin tarayya Abuja, ba kawai kashe wani da ke zargin mai garkuwa da mutane aka yi ba, har ma farfasa motar 'yan sanda aka yi, lokacin da 'yan sandan suka yi kokarin shiga lamarin.
Abin da ake bukata shi ne tattaunawa da kuma cimma yarjejeniya kan matakan magance lamarin tare da dukkan matakan gwamnati, a maimakon tsayin dakan da aka yi kan batun Amotekun da ke dauke hankalinsu daga yakar barayin da ke ci gaba da samun nasara.