An dawo da muryar malamin da ya yi zamani da Fir'auna

An sake samar da sautin muryar wani tsohon malamin addinin Kirista da ake kira Nesyamun a matsayin sautin murya mai kama da kakarin mutuwar raguna.

Ya rayu ne a lokacin dambarwar siyasar zamanin Fir'auna tsakanin shekarun 1069 zuwa 1099.

A matsayinsa na shehun Malami a Thebes, Nesyamun na bukatar murya mai ƙarfi don ayyukansa na al'ada, wanda ya shafi rera waƙa.

Lokacin da ya mutu, muryarsa ta yi nukusani, amma shekaru 3,000 baya sai gashi ƙungiyar masu binciken da suka yi wannan gagarumin aiki sun sake dawo da ita duniya.

Sun yi hakan ne ta hanyar samar da akwatin muryar da aka buga na fasahar 3D wanda aka sanya masa ma'anar murfin Nesyamun.

Ta yin amfani da muryar waka tare da sautin wucin gadi na mutum, sun kirkiri wani sauti da aka yi amannar yana kamanceceniya da muryar Nesyamun.

An yi imanin cewa wannan aiki shi ne irinsa na farko da aka samu nasarar sake farfado da muryar mutum bayan gushewarsa daga doron duniya.

Nan gaba, masu binciken suna fatan yin amfani da na'urorin kwamfuta don sake samar da hanyar hada cikakkun jimloli da muryar mamacin.

An buga sakamakon binciken wanda masana a Jami'ar Royal Holloway dake London suka gudanar da hadin guiwar jami'ar York da gidan adana kayayyakin tarihi na Leeds a mujallar kimiyya ta Scientific ''Reports journal'.'

Hanyoyin da aka bi wajen sake samar da muryar, "sun ba mu dama ta musamman don jin sautin wani da ya mutu tsawon wani lokaci da ya gabata", in ji Joann Fletcher, marubucin nazarin, kuma farfesa a fannin kimiyya na Jami'ar York.

Farfesa Fletcher ya shaida wa BBC cewa ana son jin ta bakin Nesyamun ne bayan mutuwarsa, wanda kuma hakan ba abu ne da ya sabawa addini ba.

"A kashin gaskiya abin da aka rubuta kenan a akwatin gawarsa, abin da yake so a yi Kenan, in ji Farfesa Fletcher, ga shi kuma mun samu nasarar cimma fatan nasa.

Ta yaya suka sake samar da muryar Nesyamun?

Kamar yadda watakila wasun ku da ke da ilimin kimiyya dai-dai gwargwado suka sani, da muryar da ake magana da ita da ake tace sauti, ana fitar da wannan sautin ne ta makogaro, wani wuri na musamman da ake kira da akwatin murya, sai dai mu mutane, muna jin sautin ne da zarar ya wuce gurbin sautin muryar.

To sai dai wani hanzari ba gudu ba, duka wannan fa na faruwa ne kawai a lokacin da mutum ke cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

Mataki na gaba ga masu binciken shi ne za su yi amfani da kwamfuta "don samar da kalmomi da kuma hada su don tashin cikakkiyar jimla mai ma'ana da muryar tasa", in ji Farfesa Fletcher.

Wanene Nesyamun?

Nesyamun ya kasance tsohon Malamin Kirista a Thebes a shekaru aru-aru can baya.

Ya kai kololuwar sani, har ta kai ga alfarmarsa ta ba shi damar ziyartar gunkin Amun da ake bautawa a Masar a wancan lokaci a fadarsa da ke Luxor.

Ya yi ta fama da wani ciwon dasashin hakori a wancan lokaci, daga bisani ya mutu bayan ya haura shekara 50 a duniya.

Ana ajiye da wasu sassan jikinsa da suka yi sura yanzu haka a gidan adana kayan tarihi na Leeds da ke Birtaniya.An sake samar da sautin muryar wani tsohon malamin addinin Kirista da ake kira Nesyamun a matsayin sautin murya mai kama da kakarin mutuwar raguna.