Kwankwaso ba shi da alkibla – Ganduje

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin dan siyasa 'mara alkibla' wanda ba shi da 'tsari'.

Kalaman na Ganduje na zuwa ne yayin wani bikin karbar wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP mabiya kungiyar Kwankwasiyya wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a ranar Laraba.

Tun bayan da kotun kolin Najeriya ta tabbatar wa da Ganduje nasararsa ne dai gwamnan ya mika goron gayyata ga 'yan hamayya kan su zo su hadu don ciyar da jihar Kano gaba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Abba Anwar ya aike wa manema labarai kan taron, Ganduje ya ce "ko a lokacin da Kwankwaso yake mulki, idan ka duba irin ayyukan ci gaban da ya samar da sauran tsare-tsarensa, za ka yadda da ni cewa bai san inda ya dosa ba a matsayinsa na shugaba. "

Sai dai wasu na ganin wadannan zarge-zargen na gwamnan tamkar martani ne kan wani bidiyo da aka ga Kwankwason na jawabi bayan hukuncin Kotun Koli, inda yake tsinuwa ga ''zaluncin'' da ya ce an yi musu.

Gwamnan na Kano ya kuma fada wa dandazon 'yan PDP din da suka koma APC cewa gwamnatinsa za ta tafi da su wajen samar da ci gaba a jihar Kano.

Ya kuma tunasar da su yadda ya taimaka wa Kwankwaso da kuma irin zaman da suka yi da shi tun zamanin mulkin soja lokacin da aka yi zaben 'yan majalisa.

BBC ta tuntubi wani na hannun daman Sanata Kwankwason, kuma tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a zamaninsa, Dr Yunusa Adamu Dangwani kan ko mai kungiyar Kwankwasiyyar za ta ce kan wadannan zarge-zarge, sai ya ce ''ai idan mafadin magana wawa ne to majiyinta ai ba wawa ba ne.''

''Su al'ummar jihar Kano ai sun iya rabewa tsakanin aya da tsakuwa. Don haka sun san wane ne Kwankwaso kuma sun san wane ne Ganduje da irin salon shugabancin kowannensu, sai a bar su su yi sharhi.

''Sannan kuma da yake maganar zaben fitar da gwanin 1999, ai yanzu yana tare da su Aminu Dabo da aka yi komai a gabansu lokacin, ya tambaye su mana idan ya manta, ai zabe ne sahihi aka yi ba wani magudi, sai dai idan sun bi son rai sun ki fadar gaskiya," in ji Dr Dangwani