Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Girman matsalar amfani da magunguna bogi a Afirka
- Marubuci, Daga Peter Mwai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
Kwararar magungunan jabu a Afirka wata babbar matsala ce a bangaren lafiya da bai kamata a kyale ta ci gaba da ta'azzara ba, a cewar wata gidauniya ta Birtaniya.
Gidauniyar Brazzaville na shirya wani taron ganawa da kasashe bakwai a Togo a makon nan domin magance matsalar.
Congo da Nijar da Senegal da Togo da Uganda da Ghana da kuma Gambiya za su tattauna kan matakan murkushe masu safarar magungunan jabun.
Sai dai ya girman matsalar take a Afirka kuma wane tasiri take da shi?
Menene adadin magungunan jabun?
A fadin duniya, cinikin magungunan jabu ya kai kusan dala biliyan 200 a shekara inda Afirka take cikin yankunan da abin ya shafa, a cewar wata kididdiga da aka fitar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce kashi 42 na magungunan jabu da aka kai musu tsakanin shekarar 2013 da 2017 daga Afirka ne.
Turai da Amurka kuma suna da kashi 21 cikin 100.
Amma ya sahihancin kididdigar?
Hukumar Lafiya ta Duniya tana da wata manhaja da ke fitar da bayanai kan hukumomin da ke sa ido a fadin duniya domin sanar da janyewar irin magungunan.
Don haka bayanan da aka fitar daga 2013 zuwa 2017 ya yi dai-dai da tsarin bayar da rahoto da sa ido a kasashe ko yankunan da abin ya shafa.
Hukumar Lafiya ta Duniyar ta ce yayin da jami'an lafiya suke kara wayewa da lamarin, adadin magungunan da ake kwacewa na karuwa don haka tana iya yiwuwa yankunan da ba a cika sanyawa ido ba na iya fitar da bayanan bogi kan girman matsalar.
Bright Simons wanda ya samar da wata manhaja da za ta gano ingancin magunguna a Ghana ya ce ba zai yiwu a samar da cikakkiyar kididdiga ba tun da ana cinikin magungunan ta barauniyar hanya.
Amma sau da dama ana kwace magungunan a shekarun baya-bayan nan abin da ke nuna girman matsalar a yammacin Afirka.
- Ivory Coast da Guinea-Bissau da Laberiya da kuma Saliyo sun kwace tan 19 na magungunan jabu a 2018
- An damke masu shigar da magungunan ta barauniyar hanya a Ivory Coast lokacin da suke kokarin shigo da tan 12 na magungunan jabun daga Ghana a 2019
- Hukumar 'yan sanda ta duniya Interpol a kasashen yammacin Afirka bakwai, ta kwace sama da tan 420 na magungunan jabu a 2017
- Kusan fiye da tan 19 na magungunan bogi aka kwace a Mali tsakanin 2015 zuwa 2018.
Kamfanin bincike na PwC ya ce yawan magungunan jabu a wasu kasashen ya kai kashi 70 cikin dari a kasashe masu tasowa irin su Afirka.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta kiyasta cewa a cikin duk magani 10, daya daga ciki musamman a kasashe masu tasowa har da Afirka, magunguna marasa inganci ne ko na jabu.
Menene illar magungunan jabu?
Bayanai daga makarantar kiwon lafiya ta aikin likita da ke London ta kiyasta cewa magunguna marasa inganci da magungunan jabu na cutar zazzabin cizon sauro na iya haddasa karin mutuwar mutane 116,000 daga cututtuka a kowace shekara a yankin kudu da hamadar Afirka.
A 2015, wani bincike da aka wallafa a (American Society of Tropical Medicine and Hygiene) ya kiyasta cewa sama da yara 122,000 'yan kasa da shekara biyar suna mutuwa duk shekara saboda rashin ingancin magungunan zazzabin Malaria a yankin kudu da hamadar Afirka.
Duk da cewa kididdiga ce, masana kimiyya sun ce rashin ingancin magungunan na daga cikin abubuwan da ke haddasa mutuwar yara 'yan kasa da shekara biyar.
Me yasa ake fuskantar kalubale wajen yaki da magungunan jabu?
A mafi yawan lokuta, ba a iya tantancewa tsakanin magungunan jabu da kuma na ainihi.
Sannan kuma rashin sa ido wajen hana sayar da irin magungunan ta intanet da kuma boyayyun wurare na kara habaka matsalar, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Akwai kuma batun farashin magungunan a kasashe marasa karfi.
"Idan magani daga wani sanannen mai sayar da shi na da tsada, mutane na gwada sayen maganin a wurin da yake da arha," kamar yadda hukumar lafiya ta WHO ta bayyana.
Rage farashin magunguna masu inganci ba shi ne maslaha ba.
Ko magungunan da ba su da tsada ma suna iya janyo kudi ga masu safarar miyagun kwayoyin matukar suna ciniki sosai.
Amma akwai maslaha ta fannin kimiyya da ake gwadawa don magance matsalar, har da manhaja da za ta taimaka wa masu amfani da wayoyin salula tantance ingancin magunguna.