PDP na son kotun koli ta sake duba hukuncin Imo

Shugaban Jam'iyyar APC na kasa Uche Secondus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, PDP ta Bukaci Alakalin Alkalan Najeriya ya yi murabus
Lokacin karatu: Minti 2

Babbar jam'iyyar hamyya a Najeriya, PDP, ta bukaci kotun koli ta sake duba hukuncin da ta yanke na zaben gwamna a jihar Imo

PDP ta nuna rashin gamsuwarta ne da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke kan zaben gwamna a jihar Imo, wanda ya sauke Emeka Ihedioha daga kujerar gwamna, ya dora Hope Uzodinma na jam`iyyar APC a matsayin wanda ya ci zaben.

A cewar jam'iyyar, hukuncin barazana ne dimokradiyyar kasar, kuma yana iya sanyawa jama'a su yanke kauna ga tsarin shari'ar kasar.

Sanata Umar Tsauri, sakataren jam'iyyar PDP na kasa, ya shaida wa BBC cewa "su kansu kuri'un da aka tantance kafin zaben basu kai yawan wadanda kotun ta ce an kada ba, wannan kadai ya isa jefa shakku a zukatan jama'a."

A cewarsa, "akwai zalunci da kura-kurai da yawa a wannan hukunci, don haka muna kira ga kotun koli ta sake duba wannan hukunci ta gyara shi."

Hukuncin kotun shi ne kololuwar hukunci a Najeriya, don haka nema ake kiran kotun a matsayin "kotun Allah Ya isa."

Masana shari'a irin su Barrister Bulama Bukarti, na cewa kotun za ta iya duba hukuncin, amma babu maganar ta mayar da dan takarar PDP ko da ta gano cewa shi ne mai gaskiya, a maimakon hakan sai dai ta dauki darasi domin gaba.

"Idan kotun koli ta yanke hukunci to ya zauna kenan, dalili kuwa shi ne dole ne ya kasance shari'a tana da iyaka, idan ba haka ba kenan za a yi ta shari'a ne shekara da shekaru babu iyaka, don haka hukuncin ya zauna'' In ji Barrister Bukarti.

Jam'iyyar PDP dai ta ce tana shakkar cewa kotun za ta iya sake yi mata irin wannan hukunci da ta kira rashin adalci idan ta zo yanke hukunci akan sauran zabukan da ta tsaida ranar litinin don yanke hukunci a kansu.

Yayin da kuma PDP ke kiran sake duba hukuncin, ta kuma yi kira ga Alkalin Alkalan kasar ya yi murabus.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Jam'iyyar ta ce ta kira taron kwamitin kolin don tattauna batun da kuma duba yadda za a bullo masa.

Tuni dai jam'iyya mai mulki ta APC ta yi na'am da hukuncin wacce ta ce ba ta taba cire tsammani ba a kotun duk da ta kwace mata kujerun da ta lashe a Zamfara na gwamna da 'yan Majalisar jiha da na tarayya.

Kuma shi kansa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Hope Uzodinma samun nasara a kotun, yana mai cewa nasarar ta al'ummar jihar Imo ce.