Gambia: An gargadi Yahya Jammeh da kada ya koma kasar

Yahya Jammeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yahya Jammeh ya mulki Gambia tsawon shekara 22

Kasar Gambia ta gargadi tsohon shugabanta Yahya Jammeh da aka hambarar da kada ya sake ya koma kasar daga gudun hijirar da yake yi a kasar Equatorial Guinea.

Wani mai magana da yawun gwamnatin kasar ya shaida wa BBC cewa ba za su iya tabbatar da tsaron lafiyar Jammeh ba idan ya dawo ba tare da izini ba.

Sai dai mai magana da yawun jam'iyyarsa ya ce zai iya komawa a kowane lokaci.

Makobtan kasar ta Gambia ne suka tilasta wa Yahya Jammeh yin gudun hijira a Equatorial Guinea bayan ya ki karbar kaye a zaben watan Disamban 2016.

Bayan ya kwaci mulki a shekarar 1994, Jammeh ya aiwatar da zabuka da dama a kasar, amma daga baya an zarge shi da cin zarafin 'yan Adam, wanda ya hada da kisan da ya saba wa doka da azabtarwa da kuma tsare abokan adawa.

An ambaci wadannan zarge-zarge a wurin taron kwamitin jin bahasi na TRRC da magajinsa Shugaba Adama Barrow ya kafa.

Sai dai Jammeh ba ya bayar da hadin kai ga kwamitin.

Ina Yahya Jammeh yake?

Mista Jammeh ya bayyana sha'awarsa ta komawa kasarsa.

Amma zuwa yanzu dai ana kyautata zaton yana kasar Equatorial Guinea, kusan kilomita 3,000 daga Gambia.

Shugaban rikon kwaryar jam'iyyar Mista Jammeh, Ousman Rambo Jatta ya ki bayyana takamaiman lokacin da hambararren shugaban zai koma kasar.

"Yana kan hanyarsa.. Zai karaso a kowane lokaci daga yanzu," ya shaida wa BBC.