Yadda aka yi garkuwa da dalibai a Kaduna

Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da sace wasu dalibai hudu na Kwalejin addinin Kirista ta Good Shepherd Major Seminary School da ke garin Kakau da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Lamarin dai ya auku ne da misalin karfe 12 da rabi na rana, a lokacin da wasu mutane da ke dauke da makamai sanye da khakin soji suka kutsa ciki makarantar inda suka fara harbi da bindigogi, wanda a karshe suka sace daliban hudu.

'Yan sandan jihar ta Kadunan sun kuma ce tuni mutanen suka tuntubi iyayen yaran, inda suka nemi kudin fansa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan a jihar DSP Yakubu Sabo ya shaida wa BBC maharan sun shige daji da daliban.

Wannan ne dai karo na biyu da masu garkuwa da mutane suka sace dalibai daga makarantarsu.

Ko a watan Oktoban 2019 sai da wasu 'yan bindiga suka sace wasu dalibai mata guda shida a makarantarsu Engravers College da ke kauyen Kakau a karamar hukumar Chikun.

Bayanai sun ce an yi awon gaba har da malaman makarantar mai zaman kanta su biyu a lokacin da 'yan bindigar suka shiga makarantar a cikin dare.