Yawan kitse a harshe na iya zama babban abin da ke haifar da matsalar bacci ta sleep apnoea

Overweight man asleep

Asalin hoton, SCIENCE PHOTO LIBRARY

Bayanan hoto, Matsalar bacci ta Sleep apnoea na iya janyo minshari mai karar gaske yayin baccin dare
    • Marubuci, Philippa Roxby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter

Wata matsalar bacci "sleep apnoea" da ke da alaka da numfashi na da nasaba da yawan kitsen da ke kan harshensu, kamar yadda wani bincike ya bayyana.

Idan masu fama da wannan mastalar suka rage kibarsu, binciken ya ce rage kitsen da ke kan harshen ne ya sa aka samu ci gaba.

Harsuna masu girma da masu kiba sun fi yawa tsakanin mutanen da kibarsu ta wuce kima.

Sai dai tawagar masu binciken na Pennsylvania sun ce sauran mutane da suke da kiba a harshe na da yiyuwar samun matsalar bacci.

Masu binciken a yanzu suna kokarin gano irin nau'ikan abincin da suke da karancin abubuwan sa kiba suke da kyau wajen rage kiba a harshe.

"Kana amfani da harshe wajen yin magana da cin abinci da kuam numfashi - menene dalilin da ya sa ake da kitse a harshe? in ji Dakta Richard Schwab na makarantar koyar da aikin likita ta Perelman da ke Philadelphia.

"Ba a gano abin da ke sa hakan ba - tana iya yiyuwa gado ne ko yanayin muhalli - amma karancin kitse a harshen ke sa dadin bacci."

Hakan na kuma iya janyo yawan jin bacci da rana wanda hakan ka iya shafar rayuwar mutum.

Irin wannan matsalar bacci ta fi faruwa ne a duk lokacin da hanci ke toshewa a lokacin bacci.

Mutanen da suke da kiba sosai ko kuma wadanda naman wuyansu ya wuce kima sun fi yiyuwar kamuwa da matsalar.

Yadda za a kaucewa kamuwa da matsalar baccin.

  • Kokarin rage kiba idan mutum yana da kibar da ta wuce kima
  • Yin bacci a barin jiki daya - yin amfani da matashi na musamman zai iya taimakawa
  • Daina shan taba sigari
  • Rage yawan shan barasa musamman kafin bacci
  • Kauracewa shan maganin bacci sai dai idan likita ya bada dama

Madogara: NHS UK

Masu binciken a makarantar koyar da aikin likita ta Perelman da ke Philadelphia sun yi bincike kan mutum 67 da ke fama da wannan matsala ta bacci kuma suke da kiba sannan suka rage kiba da kashi 10 cikin dari, sun samu ci gaba da kashi 30.

Masu binciken sun duba yadda tsarin kafofin iskar mutanen suke kuma ta haka suka gano abin da ke sa sauye-sauyen da kuma ci gaban.

Rage kibar ya kuma sa raguwar jijiyar habar mutum wadda ke kula da tauna, wanda shima hakan ya taimaka.

"A yanzu da muka san cewa yawan kitse a harshe na iya haifar da wannan matsala kuma matsalar baccin ta sleep apnoea na gyaruwa idan kitsen ya ragu a harshe," in ji Dakta Schwab.

An wallafa binciken a mujallar matsalolin numfashi ta American Journal of Respiratory and Critical Care Medicine.