Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Har yanzu Zidane na son sayar da Bale, Fellaini zai je West Ham
Har yanzu Real Madrid na son sayar da Gareth Bale duk da wakilinsa ya ce da wuya yabar kungiyar.(Telegraph).
Masana kwallon kafa na ganin cewa mai horar da kungiyar Zinedine Zidane ne baya sha'awar dan wasan.
Mai horar da West Ham David Moyes zai kawo dan wasan tsakiyar Beljiyom Maroune Fellaini daga kungiyar Shandong Luneng (Sky Sports).
Chelsea da Tottenham na yunkurin sayen dan wasan gaban Faransa Thomas Lemar a matsayin aro daga Atletico Madrid har zuwa karshen kakar wasannin bana.(Telegraph).
A wata mai kama da haka kuwa Tottenham na duba yiwuwar kulla yarjejeniya da Moussa Dembele na Lyon, ganin cewa Harry Kane ba zai dawo jinya ba har sai watan Afrilu.(Goal).
Leicester da Manchester City na neman mai tsaron bayan Juventus Merih Demiral mai shekaru 21.(Mirror).
Haka ma Barcelona da Arsenal na rububin sayen mai tsaron bayan RB Leipzig Dayot Upamecano. (Express).
Ita kuwa Arsenal ta shiga sahun kungiyoyin da ke son sayen mai tsaron bayan kungiyar Coritiba da ke Brazil wato Yan Couto.(Metro).
West Ham za ta karbi aron Gedson Fernandez daga Benfica da ke focugal.(Mail).
An bukaci Newcastle da ta biya sama da fam miliyan 22 idan tana son sayen matashin dan wasan Ingila Ademola Lookman da ke wasa a RB Leipzig.(Northern Echo).
Haka ma Newcastle din ta taya dan wasan gaban Najeriya Emmanuel Dennis da ke wasa a Club Brugge na Beljiyom (Daily Star).