Ludacris ya zama dan kasar Gabon

Ludacris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ludacris ya lashe kyautar mawaka ta Grammy har sau uku
Lokacin karatu: Minti 4

Mawakin 'rap' bakar fata kuma mai fitowa a fina-finai Ludacris shi ne fittacen Ba'amurke da ya zama dan wata kasa a nahiyar Afirka a baya-bayan nan.

Ludacris, wanda sunansa na asali Christopher Brian Bridges, ya yi bukukuwan Kirsimeti da na shiga sabuwar shekara a kasar Gabon, inda ya karbi shaidar zama dan kasar.

Matar Ludacris wato Eudoxie Mbouguiengue 'yar Gabon ce.

An ga mawakin dauke da takardarsa ta fasfon kasar Gabon a wani bidiyo da aka wallafa a Twitter.

A cikin bidiyon mawakin ya ce mahaifiyarsa tare da 'ya'yansa mata biyu sun karbi takardunsu na shaidar zama 'yan karamar kasar mai arzikin mai da ke yankin tsakiyar Afirka.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

A shekarun baya-bayan nan dai an samu karuwar taurari Amurkawa 'yan asalin Afirka da suka karbi takardun shaidar zama 'yan kasahen Afirka.

Wasunsu kuma sun ziyarci wasu kasashe a nahiyar domin gano asalinsu.

A watan Agustan shekarar 2019 ne dan wasa kuma Frodusan Samuel L Jackson ya karbi takardar fasfonsa na kasar Gabon bayan shugaba Ali Bongo ya karbi bakuncinsa. Mahaifin shugaban wato Omar Bongo ya mulki Gabon na tsawon fiye da shekara 40.

Bayan Gabon, wasu kasashen Afirka ma sun karbi wasu Amurkawa 'yan asalin Afirka a matsayin 'yan kasashensu.

A watan Mayun shekarar 2019, mai barkwanci kuma 'yar wasa Tiffany Haddish ta je kasar Eritrea, inda ta samu shaidar zama 'yar kasar.

Sai dai wasu sun soki matakin nata a matsayin amincewa da mulkin kama karya a Eritrea.

Haka kuma a watan Nuwamban bara, Ghana ta yi bikin bai wa Amurkawa da 'yan kasashen Caribbean 'yan asalin Afirka 126 shaidar zama 'yan kasar.

Hakan ya faru ne a yayin bikin da kasar ta yi na cika shekara 400 da dawowar 'yan Afirka na farko daga Amurka ta Arewa, wadan aka bautar.

'Afirka na cikin jinina'

Wani kamfanin binciken tsaro da ya mallaki adadi mafi girma na bayanan tsaron 'yan asalin Afirka mai suna African Ancestry a Amurka ya gano cewa galibin Amurkawa 'yan asalin Afirka na hankoron gano tushensu da silsilar danginsu.

Cinikin bayin da Amurka ta yi a Afirka wanda aka yi jigilar 'yan Afirka miliyan 12.5 zuwa Amurka a matsayin bayi, ya sa mutanen rasa asalinsu.

Hakan ya taimaka wajen shafe tarihinsu a tsawon shekara 400.

"Kakanninmu ba su taba debe tsammani ba. Ba za ku iya dankwafe tunaninmu ko ruhinmu ba. Sun ba ni kwarin gwiwar in koma", kamar yadda Ludacrs ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Kauce wa Instagram, 1
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

Presentational white space

A wani hoto da Ludacris ya dauka a gaban wani wurin jibge bayi da Turawa suka gina a Cape Coast da ke Ghana, Ludacris ya bai wa kyamara baya, sanye da wata riga da a bayanta aka rubuta: "Ni ba dan Afirka ba ne saboda an haife ni a Afirka. Ni dan Afirka ne saboda Afirka na cikin jinina. Na dawo."

Wannan wani take ke na shirin kasar Ghana na "Year of Return."

Komawa 'gida'

Samuel L. Jackson ya zabi karbar shaidar zama dan kasar Gabon bayan gwajin kwayoyin halittarsa a wani shirin bincike na musamman da Amurka ke yi na bayyana tarihin iyalan fitattun taurari, mai suna 'Gano Asalinka' (Finding Your Roots).

Shirin ya gano cewa Samuel L Jackson dan asalin kabilar Benga ne da ke Gabon.

Samuel L Jackson ya ziyarci Gabon a watan Agustan 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Samuel L Jackson ya ziyarci Gabon a watan Agustan 2019

Tsohon dan wasan na Amurka ya wallafa hotuna da dama na kasar Gabon, ciki har da wanda ya dauka tare da Sarkin al'ummar Benga.

"Yayin da kake kan hanyarka ta gano asalinka kuma hakan ta bayyana karara!" ya rubuta.

Kauce wa Instagram, 2
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2

Presentational white space

Gwamnatin Ghana ta kaddamar da shirin "The Year of Return" ne domin karfafa wa Amurkawa 'yan asalin Afirka da sauran bakaken fata mazauna kasashen waje gwiwar komawa "gida".

"Isowar 'yan Afirka da aka bautar a Arewacin Amurka ya dawo mana da jimami da bakin cikin danginmu da aka dauke daga Afirka da karfin tuwo, aka jefa su cikin muzgunawa da azabtarwa na tsawon shekaru," inji shafin shirin na intanet.

Shirin na alfahari da "karuwar jajircewar" 'yan Afirka wadanda cinikin bayi ya shafa ya kuma "warwatsa su sannan ya raba su da gidajensu" a nahiyoyin duniya.

'Dawo da martabarmu'

Da dama daga cikin taurarin bakar fata sun yi bikin shiga sabuwar shekarar nan ne a Ghana.

Shahararriyar 'yar wasa Naomi Campbell da 'yar wasa Lupita Nyong'o da mawaki Akon da kuma mahaifiyar fitacciyar mawakiya Beyonce Tina Knowles Lawson, na daga cikin manyan taurari da suka halarci bikin murnar dawowar 'yan Afirka gida 'Afrofest'.

A lokacin gagarumin bikin da aka yi a watan Nuwamba ne malamin addinin Yahudu Kohain Halev, wanda Ba'amurke ne dan asalin Afirka ya dunkule matsayin samun takardar shaidar zama dan kasar Afirka ke nufi a cikin bayaninsa.

"Abu mafi daraja da aka kwace mana shi ne asalinmu da dangantakarmu; yin hakan kamar yanke mahaifa ne".

Sai dai ya ce samun takardar shaidar zama dan kasar Ghana ya warkar da wannan ciwo: "Asalinmu da martabarmu da kuma tinkahonmu da muka rasa duk sun dawo".

Bayanan bidiyo, Amurkawa da ke dawowa Ghana

Yawancin Amurkawa 'yan asalin Afirka ba sa daukar kansu cikakkun 'yan Amurka, a cewar Dwayne Wong, wani kwararren marubucin tarihin Afirka da na 'yan Afirka mazauna wasu kasashe.

Mista Wong ya yi imani cewa daruruwan shekarun da aka kwashe ana nuna wa 'yan asalin Afirka bambamci da fifiko da kuma gwagwarmayar neman amincewa da samun karbuwa da ya ki ci ya ki cinyewa.

Kungiyoyi irin su "Black Lives Matter" masu rajin kare bakaken fata ya sa Amurkawa 'yan asalin Afirka fahimtar cewa su ba cikakkun 'yan Amurka ba ne.

Ga wasunsu kuma, samun takardar shaidar zama dan kasar Afirka ko kuma gano asalinsu da wasu kabilun Afirka, na iya zame masu muhimmin abu na gano asalinsu.