Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu shan taba na kokawa da matsanancin ciwo a jikinsu
- Marubuci, Daga James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
Wani rahoto ya ce mutanen da ke shan taba sigari da kuma wadanda suka daina sha sun bayyana irin yadda suke kasancewa cikin ciwo fiye da mutanen da basu taba shan tabar ba.
Binciken da aka gudanar ya dogara ne da nazarin bayanai daga sama da mutane 220,000 wanda jami'ar UCL da ke birnin Landan ta gudanar.
Masu binciken sun ce ba a san dalilin hakan ba amma kuma ba zai wuce nasaba da shan taba sigari ba da ke haifar da sauye-sauyen din-din-din a jikin dan adam.
Wata kungiya mai yaki da shan taba sigari, Ash ta ce bai kamata binciken ya zo da mamaki ba saboda illolin taba sigari.
Masana kimiyya suna nazari kan bayanan da aka tattaro daga kafafen sada zumunta a dakin binciken BBC tsakanin shekarar 2009 da 2013.
An raba mutanen da aka yi nazarin a kansu zuwa kashi uku:
- Wadanda suke shan taba sigari kowace rana
- Wadanda a baya suke sha kowace rana
- Wadanda a yanzu suke shan taba sigarin duk rana
An bukaci mutanen su fadi irin ciwon da suka kasance a ciki sannan aka mayar da abin da suka fada zuwa ma'auni daga 0 zuwa 100.
Wadanda suke da maki mai yawa su ne suka kasance cikin tsananin ciwo.
Masu shan taba sigarin da kuma wadanda suka daina sha sun fi jin ciwo kan wadanda basu taba shan tabar ba, kamar yadda binciken da aka wallafa a mujallar Addictive Behaviours ya nuna.
Ma'ana dai shan taba sigari yana da alaka da ciwon da mutane masu shan taba ke ji a jikinsu ko da kuma masu shan sun bar dabi'ar.
''Babban abin da binciken ya gano shi ne wadanda suka daina shan taba har yanzu suna fuskantar ciwo'' a cewar daya daga cikin masu binciken a jami'ar UCL, Dakta Olga Perski.
Ta kara da cewa ''mutanen da aka yi nazarinsu suna da yawa kuma zamu iya bugar kirji mu ce akwai abin da ke faruwa anan.''
''Amma ba za mu iya cewa ko hakan na da wata ma'ana a asibiti ba.''
Dakta Perski ta ce wani abin mamaki da binciken ya gano shi ne irin tsananin ciwon da wadanda suke shan taba masu karancin shekaru tsakanin shekara 16 zuwa 34 suka fi ji a jikinsu.
Me ke faruwa?
Babu wani bayani kan abin da ya sa hakan ke faruwa.
Wani ra'ayi da aka gabatar shi ne dayawa daga cikin dubunnan sinadaran da ke cikin hayakin taba na iya lalata naman jikin dan adam har tsawon rayuwarsa, abin da zai haifar da ciwo.
Wani abin kuma shi ne shan taba sigari na iya haifar da illa ga tsarin kwayoyin halittar dan adam
Wannan ya ta'allaka ne kan abin da mutane ke ji idan suna jin zafi.
Sai dai akwai yiwuwar cewa shan taba sigari alama ce amma ba abin da ke haifar da tsananin ciwon ba.
Misali, wasu bincike sun alakanta yanayin halayyar dan adam da yadda mutanen ke jin radadin zafi da kuma hadarin shan taba sigari.
Za a iya cewa, mutumin da zai iya bayyana irin radadin da yake ji shi ne wanda ake iya ganin zai fara shan taba sigari.
Dakta Perski ta bayyana cewa ''wannan wani abu ne da ya kamata a yi duba a kai.''
Sai dai ta kara da cewa binciken da suka yi na baya-bayan nan ya yi dai-dai da binciken da suka yi a baya wanda ya danganta shan taba sigari da matsanancin ciwo da kuma ciwon baya.
''Ko da ka daina shan taba sigari, dadewar da ka yi kana sha na iya haifar da ciwo, abu ne mai kyau mutum ya daina shan tabar tun kafin lokaci ya kure,'' kamar yadda Dakta Perski ta shaida wa BBC.
Babbar jami'ar kungiyar da ke yaki da shan taba sigari ta Ash, Deborah Arnott ta ce ''an gano alamar da ke nuna shan taba sigari na haifar da ciwon huhu a shekarun 1950 kuma tun lokacin aka gano cewa shan taba sigarin na iya haifar da wasu cututtukan.''
''Hakan ya hada da cutar daji da ciwon zuciya da matsalar numfashi da makanta da ciwon siga da mayar da mutum kurma da cutar mantuwa da rashin haihuwa.
Masu shan taba sigari suna daukar tsawon lokaci kafin su warke daga tiyata kuma akwai yiwuwar sakamakon aikin da aka yi musu ya lalace.
''Don haka ba abin mamaki bane cewa masu shan taba sigari ma suna shan wahala fiye da wadanda ba u taba shan tabar ba.''