EFCC ta kama tsohon ministan shari'ar Najeriya Bello Adoke

Asalin hoton, @officialEFCC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke tsohon ministan shari'ar Najeriya Mohammed Bello Adoke jim kadan bayan saukarsa a kasar daga Dubai.
Kamar yadda hukumar ta sanar, 'yan sandan kasa-da-kasa na Interpol ne suka taso keyar Adoke tare da yi masa rakiya har Abuja.
"Shugaban EFCC Ibrahim Magu da kuma mahukuntan Dubai sun dade suna tattaunawa game da tsohon ministan shari'ar," in ji EFCC.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Tun a safiyar ranar Alhamis ne aka samu rahoton isowar Bello Adoke Najeriya , inda jami'an EFCC suka yi jiran saukarsa a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Mohammed Bello Adoke ne Ministan Shari'a kuma babbban lauyan Gwamnatin Tarayyar Najeriya a zamanin mulkin Goodluck Jonathan.
Tun a shekarar 2017 ne EFCC ta fara tuhumar Adoke da kamfanonin mai na Malabu Oil & Gas Limited da Shell da Agip da wasu mutanen da dama da zargin almundahana.
A ranar 17 ga watan Afrilun 2019 ne wata babbar kotu a Abuja ta bayar da umarnin cafke shi sakamakon gaza gurfana a gabanta.







