Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Gwamnan Kano zai iya tubewa da nada sarki bisa radin kansa'
Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ki amincewa da bukatar masu zaben sarki a Kano na sabunta hanin da ta yi wa gwamnan jihar da kada ya saka baki cikin aikin masu zaben sarkin ba tare da ya tuntube su ba.
Wannan ya biyo bayan wata kara da masu zaben sarkin suka gabatar a gaban Mai shari'a Ahmed Tijjani Badamasi na babbar kotun jihar da ke sakatariyar Audu Bako a Jihar ta Kano a makon da ya gabata.
Umarnin kotun na makon jiya ya hana gwamnan daukar duk wani mataki kan sarkin Kano ko amfani da sabuwar dokar masarautun Kano da aka kafa kwanannan.
Lauyoyin gwamnati na cewa umarnin kotun na nuna cewa gwamna zai iya sauke sarki ko kuma ya nada shi ba tare da tuntubar masu zaben sarkin ba.
To sai dai har yanzu batun yana gaban kotun kuma za a fara sauraron ainihin karar ranar 20 ga watan nan.
Wannan hukuncin na kotu na zuwa ne bayan da sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Ci gari da Sarkin Ban Kano, Alhaji Mukhtar Adnan, wadanda suna daga cikin masu zaben sarkin kano.
Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin hakan ka iya kara haddasa tsamin dangantaka tsakanin bangaren gwamnanti da kuma masarautar ta Kano.
Umarnin kotun na ranar 10 ga Disamba ya zo ne kwana biyu bayan gwamna Ganduje ya nada Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan jihar tare da umartar sarkin ya kira taron majalisar ba tare da bata lokaci ba.
Wasu na ganin matakin da gwamnan ya dauka a matsayin kokarin gyara alaka tsakaninsa da masarautar ta Kano.
To amma masu lura da al'amura na ganin matakin a matsayin daure Sarki Sanusi da jijiyar jikinsa.
Sai dai wasu masu kusanci da fadar na cewa fadar ba ta samu sanarwar nada Sarki Sanusi a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan jihar a hukumance ba.
Hukuncin na kotu dai ya kuma hana gwamna yin wani aiki da bisa al'ada masu zabar sarkin Kano ke yi, har sai kotun ta saurari karar da aka shigar gabanta.