Pakistan: An yanke wa Pervez Musharraf hukuncin kisa

Asalin hoton, Reuters
An yanke wa tsohon Shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf hukuncin kisa.
Wata kotu ta musamman a kasar ce ta yanke wa Musharraf hukuncin saboda samun sa da laifin cin amanar kasar.
Musharraf shi ne tsohon shugaban mulkin soja na farko da aka kama da aikata manyan laifuka a kasar.
Laifukan tsohon shugaban sun hada da jingine tsarin mulkin kasar da kuma sanya dokar ta-baci a kasar a shekarar 2007.

Asalin hoton, HANDOUT VIA GETTY
A 1999, Musharraf ya yi juyin mulki a Pakistan inda ya ci gaba shugaban kasar daga 2001 zuwa 2008 lokacin da ya yi murabus daga mukamin.
A watan jiya ne alkalai uku na kotun suka yanke hukuncin, amma babbar kotun kasar ta hana su bayyana hukuncin.
Tun a shekarar 2016 Janar Musharraf ke zaune a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa inda yake jinya don haka an yanke wannan hukuncin ne a yayin da yake wajen kasar.







