Yadda aka aurar da 'yan mata 'yan hudu

Asalin hoton, Uthara
- Marubuci, Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Amaren 'yan uwan juna su hudu sun fito ne daga jihar Kerala da ke kudancin kasar India.
An haife su a rana guda, sun tashi a gida daya daki daya, kana tare suke cin abinci, haka sutura ma iri daya suke sanyawa.
A makaranta ma, wajen zamansu guda har sai da suka kai shekara 15.
A yanzu kuma, za su amarce a rana guda.
Amaren suna da dan uwa namiji guda wanda aka haifesu a rana guda shi ma.
Amaren sun bayyana wa BBC yadda rayuwarsu ta kasance tun bayan haihuwarsu.
Tarihin yadda rayuwarsu ta kasance
An haife su 'yan uwan junan wato Uthra da Uthraja da Uthara da Uthama da kuma dan uwansu namijin Uthrajan, a ranar 18 ga watan Nuwambar 1985.
Yanzu suna shirin amarcewa a rana guda a ranar 26 ga watan Afrilun 2020.
Uthara, ta ce, yanzu ba bu abin da suke illa shirye-shiryen biki, inda ta ce har yanzu ba su sayi kayan da za su saka ba a ranar bikin ba, amma ta san cewa kaya iri daya za su saka.

Asalin hoton, Uthara
Uthara, 'yar jarida ce, kuma wanda za ta aura ma dan jarida ne.
Za ayi auren ne bisa yadda al'adarsu ta tanada, kuma mahaifiyarsu ce ta taimaka musu wajen zabar mazajen da za su aura.
A watan Satumbar 2019, aka yi musu baiko, to amma daya daga cikin mazajen amaren bai samu damar halatta ba saboda yana aiki ne a gabas ta tsakiya.
A yanzu amaren wadanda 'yan biyar ne amma kuma ba sa kama da juna, na kokarin ganin sun tanadi duk abin da za a yi amfani da shi iri daya.

Asalin hoton, Uthara
Uthraja, ta yi zarra a karatu, ita kuwa Uthama, kade-kade da raye-raye ta ke so, hakan ya sa ta koyi kidan goge wato Violin.
Dan uwansu namijin Uthrajan, shi ma wani kida na Tabala ya ke so, shi ya sa ma yaje ya koyi yadda ake yi.
Uthra kuwa zuwa ta yi ta koyi bangaren zayyana tufa.
Uthraja da kuma Uthama, sun zamo wadanda sukan yi allurar da ke sanya bacci ko disashe jin zafi a yayin tiyata.
A lokacin da suka ce su na son yin aure, Uthraja ce ta fara samun miji, amma kuma sai ta ce su dan jira 'yan uwanta tukunna suma su samu miji don hada su ayi bikin su tare.
Uthraja, ta shaida wa BBC cewa, burin mahaifiyarsu shi ne taga ta aurar da 'ya'yan nata rana guda, don haka ne ta ce su dan jira 'yan uwan nata.
Ana dai yawan kashe makudan kudade a wajen shirya biki a India, hakan ya sa yawancin iyalai da dama kan hada auren 'ya'yansu da 'yan uwansu.
Wannan ya sa 'yan uwan junan su hudu suka ce gara a hade bikinsu, maimakon a raba, saboda suna tausayin mahaifiyarsu wajen kashe kudade.
To sai dai kuma a bangaren Uthraja, wanda za ta aura baya son auren gaggawa.

Asalin hoton, Uthara
Uthrajan, za ta auri Akash Kumar ne, wanda shi ma yake aikin masu allurar sanya bacci ko dasashe radadi a yayin tiyata a gabas ta tsakiya.
Ta ce, a da muna aiki ne a asibiti guda, kafin daga bisani ya koma Kuwait.
Muna san junanmu, haka iyayensa sun ji dadi da suka ji muna son juna har muna so muyi aure, hakan ya ba su damar tunkarar mahaifiyarmu, inji Uthrajan.
Tana son ta cika shekara biyu cif da fara aiki a asibitin da take aiki, kafin ta bi mijinta zuwa Kuwait bayan aure.
Ta ce 'abin damuwar a nan shi ne, ban taba zuwa wata kasaba, haka ban taba nisa da mahaifiyata da kuma 'yan uwana ba, amma kuma duk da haka ina son naga nayi aure'.
Uthraja ta ce tana fatan ta samu aiki cikin sauki a Kuwait, kuma 'yar uwarta Uthama ma wanda za ta aura aiki ya ke a gabas ta tsakiya.
'Yan biyar dina masu faranta mini rai

Asalin hoton, Uthara
Iyayen yaran sun yi farin ciki a lokacin da aka haifesu su biyar.
Sun sanya musu suna "Pancharatna", ma'ana 'yan biyar dina masu faranta mini rai.
Yaran sun yi karatu sosai domin sun kasance masu hazaka, to amma batun lafiyarsu ce abar damuwa.
A lokacin da aka haifesu ba su da girma, kuma ba su da cikakkiyar lafiya, domin suna yawan rashin lafiya, inji mahaifiyarsu Rema Devi.
Iyayensu Prema Kumar da Rema Devi, sun sha gwagwarmaya wajen rainon yaran biyar.

Asalin hoton, Uthara
Suna da rarar kudi kadan, hakan ya sa suka mayar da hankalinsu wajen karatu.
A India, a kan fifita 'ya 'ya maza a wasu gidajen, amma kuma su wadannan 'yan biyar din, sun ce iyayensu duk daya suka dauke su, ba bu wanda ya fi wani a cikinsu.
Mahaifiyarsu ta ce, ba ta taba kirkirar wata matsala a tsakanin 'ya'yan nata ba, inda Uthara ta ce har kayan junan mu muna sa wa.

Asalin hoton, Uthara
Wani babban tashin hankali ya same su a shekarar 2004, lokacin da mahaifinsu ya kashe kansa, saboda durkushewar da shagonsa ya yi, a lokacin yaran suna da shekara tara.
Bayan mutuwar mahaifin na su, sai 'yan jarida suka buga labarin iyalan hakan ya sa gwamnatin kasar ta ba wa mahaifiyarsu aiki a wani banki da ke garinsu.
Rema ta ce, aikin da aka ba ta ya taimaka mata wajen renon 'ya'yanta da sai musu abinci da kuma biyan kudin makarantarsu.

Asalin hoton, Uthara
Wani likita a unguwarsu shi ne ya basu gidan da suka zauna.
Rema ta ce, yaranta biyar sun yi kokari a bangaren karatunsu, kuma dukkaninsu sun kammala jami'a.
Uthara ta ce, yanzu mahaifiyarsu na cikin farin ciki, kuma a ko da yaushe ta na so su zamo masu dogaro da kansu.

Asalin hoton, Uthara
Za dai a gayyaci 'yan uwa da abokan arziki ne a wajen bikin wadannan 'yan mata.
Ba kasafai ake samun 'yan biyar ba, hakan ya sa 'yan jarida na kasar India ke bibiyar rayuwar wadannan yara tun da aka haifesu, wannan ya sa suma 'yan jaridar za su halacci bikin.
Wani abin tausayi
Wadannan yara 'yan biyar, yanzu sun fara tunani a kan yadda za su rinka taimakon mahaifiyarsu.
Sannan sun ce, ba za su taba rabuwa da juna ba.
Suka ce koda mun kasance aure ya rabamu, to akoda yaushe zamu rinka tuna juna tare da tuntubar juna muna jin halin da kowaccenmu ke ciki.











