Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yau ake babban zabe a Burtaniya
Miliyoyin mutane za su kada kuri'a a babban zabe na uku cikin shekaru biyar a Burtaniya.
Zaben, wanda irinsa ne na farko da aka fara yi a watan Disamba cikin kusan shekaru 100, ya biyo bayan na 2015 da 2017.
An bude rumfunan zabe cikin mazabu 650 a fadin Ingila da Wales da Scotland da Arewacin Ireland da karfe 07:00 dai-dai agogon GMT.
Da zarar an rufe rumfunan zabe da karfe 10:00 agogon GMT, za a fara kirga kuri'un. Za a bayyana sakamakon zaben da safiyar Jumma'a.
Gaba daya 'yan majalisa 650 ne za a zaba a kowace mazaba.
A shekarar 2017, mazabar Newscastle ta Tsakiya ita ce ta fara bayyana sakamakon zabenta awa guda bayan da aka gama kada kuri'u.
A al'adance, ana gudanar da zabe ne a Burtaniya duk shekara hudu zuwa biyar.
Amma a watan Oktoba, 'yan majalisa sun kada kuri'a don a gudanar da zabe cikin gaggawa.
Wannan zaben shi ne na farko da aka yi a lokacin hunturu tun shekarar 1974 kuma na farko a watan Disamba tun 1923.
Duk wani da ya kai shekara 18 ko fi ya cancanci yin zaben, muddin 'yan kasar Burtaniya ne ko kuma dan wata kasar Commonwealth, wanda ya cika wasu sharudda ko kuma dan Jamhuriyar Ireland sannan sai ya yi rajistar yin zabe.
An rufe yin rajistar ran 26 ga Nuwamba.
Ana iya samun bayanai kan inda za ayi zabe a kan shafin intanet na Hukumar zabe sannan an jera su kan wasu katuna da aka aika gidaje. .
Firayim Minista Boris Johnsin ya kada kuri'arsa- ya ziyarci wata rumfar zabe a garin Westminster, tare da karensa Dilyn.
Kafin zaben, hukumar da ke sa ido kan zaben ta sanar da cewa an haramta daukar hoton 'selfie' da ma sauran hotuna a rumfunan zabe kuma yin hakan na iya zama saba wa ka'ida. .
Hasashen yanayi na BBC ya nuna cewa za a sheka ruwan sama ran Alhamis a sassan kasar da yawa, kuma za a yi sanyi sosai a biranen Edinburgh da Cardiff da Belfast da London.