Shugaba Buhari zai tafi Masar

Lokacin karatu: Minti 1

Shugabn Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi garin Aswan na kasar Masar ranar Talata domin halartar wani taron zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka.

Kamar yadda fadarsa ta bayyana a shafinta na Twitter, shugaban zai shafe ranakun Alhamis da Juma'a yayin taron.

Ta kara da cewa taron, wanda aka kira shi da suna "An Agenda for Sustainable Peace and Development in Africa", wani yunkuri ne da nahiyar Afirka take yi na nemo wa kanta hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro da kuma cigaba.

Wannan ne balaguro na 12 zuwa wajen Najeriya da Buhari zai yi tun bayan cin zabensa a karo na biyu.

Tafiye-tafiyen Buhari bayan cin zabe:

30- 2 Yuni - Saudiyya - Taron kungiyar kasashen musulmai

6-2 Yamai - Taron Tarayyar Turai kan kasuwancin bai daya

26 Yuli -Liberia - Bikin samun 'yancin kai

25-30 -Japan - Taro kan alakar Tokyo da Afirka

14 Satumba - Burkina Faso - Taron ECOWAS kan ta'addanci

25 Satumba - 1 Oktoba - New York City - US - Ziyarar aiki.

2-3 Oktoba - Pretoria - Afirka ta Kudu - Ziyarar aiki

21-23 Oktoba - Sochi - Rasha

28 - 31 Oktoba - Riyadh - Saudiyya - Taron kasuwanci

31 - 17 Nuwamba - London - Burtaniya - Ziyara don kai

28 - 29 Nuwamba - Malabo, Equatorial Guinea - ziyarar aiki