Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A rika biyan marasa aiki albashi a Najeriya – Sanatoci
Majalisar Dattawa a Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakan gaggawa a kan matsalar rashin yi aiki a tsakanin 'yan kasar.
A mahawararsu a kan kudurin da Ike Ekweremadu ya gabatar kan matsalar rashin aikin yi a yau Laraba, sanatocin sun ce gazawar gwamnati wurin samar wa 'yan kasa ayyuka na da matukar hadari.
'Yan Majalisar na kuma neman gwamantin ta kafa asusun tallafa wa 'yan kasar marasa aiki zuwa lokacin da za su samu aikin yi.
Sun kara da cewa da yawa daga cikin matasan kasar da suka kammala karatu ba su da aiki.
Majalisar ta bukaci dukkan matakan gwamantin kasar su sanya dokar ta-baci a kan rashin aiki yi tsakanin al'umma, musamman matasa. Sannan a bude shirin samar da ayyukan yi ga matasa karkashin ma'aikatar tsare-tsare ta kasa.
Bayan haka ya kamata gwamanti ta bai wa kamfanonin 'yan kasuwa damar yin aiki ba tare da matsi ba, ta yadda za su iya daukar matasa aiki, kamar yadda sanatocin suka yi kira.