Tokyo 2020: An haramta wa Rasha wasanni har shekara hudu

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar hana ta'ammali da kwayoyi masu kara kuzari yayin wasanni, Wada, ta haramta wa kasar Rasha yin dukkan wasu wasanni har na tsawon shekara hudu.
Hakan na nufin Rasha ba za ta shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2022 da za a yi a Qatar ba da kuma gasar guje-guje da tsalle-tsalle da za a yi a Tokyo a 2020.
To sai dai masu guje-gujen da tsalle-tsallen da za su iya nuna shaidar rashin shan kwayoyi masu kara kuzari za su iya shiga gasar amma ba da sunan Rasha ba.
Hukumar ta Wada ta yanke hukuncin ne yayin wani taron shugabanninta a Lausanne na kasar Switzerland.
Wannan hukuncin dai na zuwa ne bayan da Wada ta nuna rashin amincewa da hukuma mai sa ido kan amfani da kwayoyin masu kara kuzari ta Rasha, Rusada bisa zargin yin magudin sakamakon gwajin da aka yi wa 'yan kasar wanda kuma aka bai wa masu bincike a watan Janairun 2019.
Yanzu dai hukumar Wada ta ce hukumar Rusada na da kwanaki 21 domin daukaka kara dangane da haramcin.
Da ma dai masu tsalle-tsalle da guje-guje 168 'yan kasar Rasha ne su ka fafata a gasar Olympics ta 2018 da aka yi Pyeongchang, ba da sunan Rasha ba.
Tun shekarar 2015 ne dai aka haramta wa Rasha shiga gasar wasanni guje-guje da tsalle-tsalle a matsayinta na kasa.
To sai dai duk da wannan harmaci, Rashar za ta shiga gasar Euro 2020











