Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me kai el-Zakzaky da matarsa gidan yari ke nufi?
- Marubuci, Badariyya Tijjani Kalarawi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
Da alamu an shiga wani sabon babi a ce-ce-ku-ce dangane da batun ci gaba da tsare jagoran kungiyar harkar Musulunci a Najeriya ta mazhabar Shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim el-Zakzaky da matarsa Zeenatu.
Ce-ce-ku-cen na zuwa ne sakamakon umarnin da wata babbar kotu a Kaduna ta bayar don mayar da su gidan yari.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis da safe, inda ta ce za a mayar da su gidan yarin ne don lauyoyinsu da likitocinsu su samu damar ganinsu cikin sauki.
Sai dai el-Zakzaky da matarsa Zeenatu ba su je kotun ba a ranar Alhamis, kuma lauyansu ya ce rashin zuwan nasu na da alaka da halin rashin lafiya da suke ciki.
Sai dai magoya bayan malamin sun yi Allah-wadai da umarnin na kotu, yayin da wasu masana fannin shari'a ke ganin kotun ta yi abin da tuni ya kamata ta yi.
Amma kuma wasu na ganin hakan zai taimaka wa malamin addinin a yayin da za a ci gaba yi masa shari'a.
Tun bayan kama jagoran na IMN da mai dakinsa a shekarar 2015 suke hannun hukumar DSS, kuma wannan ne karon farko da aka kai su gidan yari.
Me hakan ke nufi ta fuskar shari'a?
BBC ta yi hira da Barista Sunusi Musa kuma ya ce kotu tana da damar ta fadi inda ya dace a ajiye wanda ake tuhuma da laifi.
''Na farko a doka abin da ya dace a yi shi ne duk lokacin da jami'an tsaro ko 'yan sanda ko wata hukuma da aka ba ta damar gurfanar da wani a gaban kotu to ta kai shi gaban kotun," Barista Sunusi ya fada.
Ya ci gaba da cewa: "Daga ranar yake fita daga hannunsu, ya koma hannun kotu, inda daga nan ne kotun za ta kai shi gidan yari.'
"Wani lokacin kotu ta kan duba wasu dalilai, ko wanda ake tsarewar kan bukaci maimakon a kai shi gidan yari gara an bar shi a hannun hukuma kamar misali hukumar EFCC ko DSS.
"Watakila yana ganin rikon da ake yi masa a wadannan wuraren an fi kula da shi, ko mutuntawa ba kamar gidan yari ba.
"A nan kotun idan ta ga dama kuma tana ganin shi ne adalci ko ya fi maslaha, to za ta iya amincewa da zamansa a wurin hukumomin, ba lallai sai an kai shi gidan kaso ba.''
Me ya sa ba a kai Zakzaky da mai dakinsa gidan yari tuntuni ba?
Barista Sunusi Musa cewa ya yi "wani lokacin kotu ta kan duba wasu dalilai, ko wanda ake tsarewar kan bukaci maimakon a kai shi gidan yari gara an bar shi a hannun hukuma kamar misali hukumar EFCC ko DSS, watakila ya na ganin rikon da ake masa a wadannan wuraren an fi kula da shi, ko mutuntawa ba kamar gidan yari ba.
Anan kotun idan ta ga dama kuma ta na ganin shi ne adalci ko ya fi maslaha, to za ta iya amincewa da zamansa a wajen hukumomin ba lallai sai an kai su gidan kaso ba.''
Anya kuwa ba wata dabara ce ta kai shi kotu, daga nan akai shi gidan kaso sai shari'ar ta bi shanun sarki ba?
''Abinda na ke so ku gane shi ne ai El-Zakzaky ya na da lauyoyi. kuma ita kotu yadda ta ke zamanta idan an zauna da lauyoyin baki daya tare da mai shari'a dan duba ranar da za a sake zaman kotun kuma ya kasance ba su da wani abu sai a daidaita kan wannan ranar.''
Amma Barista Bulama Bukarti lauya mai zaman kan sa da ke karatun digirin-digirgir a Birtaniya na da ra'ayin wannan umarni na kotu zai taimakawa shari'ar da ake yi wa El-Zakzaky ta hanyoyi da dama.
''Hanya ta farko zai bai wa lauyoyinsa damar ganawa da shi a kowanne lokaci suka so babu shamaki a duk lokacin da suke so, saboda gidajen yari su na bai wa lauyoyi damar ganin wanda suke karewa su gana da shi a tun daga ranar Litinin har zuwa Lahadi. Hakan zai ba shi damar shaidawa lauyoyin wasu bayanai da suke bukata. Daman tun da fari akwai korafin da lauyoyi da 'yan uwa har da abokai suka shigar na rashin ganawa da shi a lokacin da ya ke hannun hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.
Anya ba za a sanya takunkumin ganinsa a gidan kaso ba?
Bulama Bukarti ya ce babu wannan takunkumin indai ba kotu ce ta bada umarni ba, tun da maganar a gaban shari'ar ta ke, ita ce ta baiwa DSS damar rike shi a hannunsu, kuma ta sake ba su damar kai shi gidan kaso.
Ya ce duk bayanan da ya karanta babu inda kotu ta ambaci takunkumi, saboda hakkinsu ne da kundin tsarin mulki da shari'a suka ba su, kuma babu wanda zai yanje musu ita.
Ko dai salon maida shi gidan Kaso na da nasaba da kokarin shiriritar da shari'ar ya ci gaba da zama a Gidan yari?
Barista Bulama ya ce ''daya daga cikin damuwar da lauyoyinsa suka nuna kenan, kuma ci gaba da tsare shi da ake yi da ma sauran 'yan Najeriya da ke tsare a gidajen kaso ba daidai ba ne, kuma ya sabawa doka. Don a tanadin kundin tsarin mulkin kasar, ya ce lallai a ba da belin wanda ake zargi da aikata wani laifi cikin watanni uku, matukar ba za a iya kammala shari'ar da ake yi ma sa ba.
''Amma idan an kula El-Zakzaky an tsare shi sama da shekaru biyu, yanzu kuma an maida shi gidan kurkuku. Tun da fari ma shari'ar ta na tafiyar hawainiya, idan shari'a ta na da hujja idan ka gama bincike babu dalilin da za a dauki watanni uku ana shari'a.
Baristan ya kuma ce ga alamu sun nuna ba'a kai ga kammala wannan shari'a ba, amma kuma an kai shi gidan kurkuku.
Ya ce ''Don haka ba Zakzaky ba, duk wani dan Najeriya da ake tsare da shi da ya wuce watanni uku ba tare an yi masa shari'a ba bai dace ba. Saboda haka ina kira ga shugabanni idan su na da shaida akan bawan Allah, ya kamata su gabatar da shaidunsu a gaban kotu, kotu ta yanke hukunci.
''Idan sun san ba za su iya ci gaba da wannan shari'ar ba, to ba daidai ba ne, zalunci ne su ci gaba da rike shi. Sannan zalunci ne a ci gaba da tsare duk wani dan Najeriya da ya wuce watanni uku ba a bada belin shi ba, ba kuma yanke ma sa hukunci ba.''
Me ya faru tsakanin Sojojin Najeriya da 'yan Shi'a?
A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2015, mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya suka hana ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janar Tukur Burutai wucewa Zaria, bidiyon yadda sojojin sukai kokarin sasantawa da 'yan Shi'a don su wuce ya karade kafafen sada zumunta.
An yi arangama tsakanin sojoji da 'yan Shi'a, lamarin da ya janyo hasarar rayuka.
Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.
Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan an yi awon gaba da wasu da dama.
Tun daga wancan lokacin ne hukumomi ke tsare da Sheikh Zakzaky da matarsa Zinatu, duk da cewa kotu ta bayar da izinin a sake su a lokuta daban daban.
Itama gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da Zakzaky gaban shari'a kan zargin kisan wani soja mai mukamin kofaral, daya daga cikin ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa na Najeriyar.
Mabiya Shi'a sun yi ta zanga-zanga a daukacin Najeriya don bukatar a saki jagoran nasu, lamarin da ya janyo taho mu gama tsakaninsu da jami'an tsaro a lokuta mabanbanta.
Bukatarsu ita ce a bai wa jagoran nasu damar tafiya asibiti kasar waje shi da mai dakinsa don yi musu magani.