Zaftarewar kasa ta binne kauyukan Kenya bayan ambaliya

People gather around the road that was destroyed by heavy rain near Kapenguria, West Pokot County

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zaftarewar kasar ta biyo bayan ruwan sama mai kama da bakin kwarya da aka yi a yankin

Jami'an gwamnati a Kenya sun ce kusan mutum 40 sun rasa rayukansu a sanadin zaftarewar kasa da ya auku a yammacin kasar.

Iftila'in ya tafi da gidaje bayan da mamakon ruwan sama ya rika sauka a yankin. Masu ceto na can suna kokarin isa yankin saboda ambaliyar ruwa ta shafe dukkan hanyoyi da gadoji.

An shafe makonni ana tafka ruwan sama a yankin gabashin Afirka, har ta kai ga ambaliyar ruwan saman ta shafe kauyuka masu yawa a Sudan ta Kudu.

An kuma sami rahotannin zaftarewar kasa da laka a Tanzania, da Habasha da Somalia, kuma masana kimiyya sun ce tekun Indiya na da duni fiye da yadda aka saba.

George Natembeya shi ne kwamishinan yankin Rift Valley na Kenya, yankin da zaftarewar kasar ta fi shafa:

"Mamakon ruwa yayi ta fadi a wata karamar hukuma mai suna west Pekot a yankin Rift Valley wanda a sanadin haka aka sami zaftarewar kasa.

Ya kuma kara da cewa: "Mutane da dama sun rasa rayukansu. Mun sami hako mamatan da tabo da laka suka binne, amma muna kokarin gano wadanda ambaliya ta tafi da gawarwakinsu."

Ya ce an kai wadanda suka tsira amma sun sami raunuka na asibiti, amma a halin da ake ciki gwamnati ta mayar da hanaklinta ne ga batun gano gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu a wannan iftila'in.

Map of Kenya showing West Pokot county and Nairobi

Shugaban Kenya Uhuru Kenyata ya bayyana jimaminsa ga iyalai da 'yan uwan wadanda wannan lamari ya shafa a kasar.

Jami'an kiwon lafiya sun ce akwai yara bakwai cikin wadanda zaftarewar kasar ta rutsa da su.

Shugaban ya umarci dakarun sojojin kasar su garzaya zuwa yankin domin bayar da taimakon gaggawa ga al'umomin da ke wurin wadanda ke neman mafaka da abinci.