Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abinci biyar masu guba da ka iya kisa
A haka, ana iya cewa babu wani hadari a tattare da abinci.
Amma maganar gaskiya ita ce, ba ko wane abinci ne ake ci ba tare da daukar mataki ba, kamar dubawa da kyau, ko wajen dafawa ko shiryawa - kamar cire wasu sassan jikin abincin da ke iya cutarwa.
Idan ba a dauki wadannan matakan ba, akwai nau'in abincin da idan aka ci suna iya janyo cuta, kuma alamomin cutar na iya zama tashin zuciya ko gushewar hankali ko ma mutuwa.
A yanayi marar kyau ko kuma abincin da ba a adana shi ko dafa shi yadda ya kamata ba, abincin na iya janyo tashin zuciya, daukewar numfashi ko gushewar hankali har ma a kai ga an mutu.
Ga nau'in abinci biyar da ya kamata a duba sosai kafin a ci. Asali ma, idan ba ku da tabbas kan wadannan nau'ukan abinci, ka da ku ci su kwata-kwata.
1. Kifin Puffer
Kifin Puffer na iya kisa.
Yana dauke da sinadarin 'tetrodotoxin', wani sinadari mai guba wanda ake tunanin ya fi sinadarin 'cyanide' hadari.
Sai dai suk da hadarinsa, ana matukar son cin Kifin Puffer a wasu kasashen.
A kasar Japan, ana cin kifin (ana kiransa fugu a can) danye ko kuma a sa a miya.
Ana horar da masu dafa abinci tsawon shekaru kafin a ba su damar dafa wa mutane kifin.
Abin dubawa shi ne a tabbatar cewa kafin a fara ci, an cire duka sassansa masu dauke da guba, wadanda suka hada da kwakwalwarsa da fatarsa da idanunsa da kayan cikinsa.
2. Cikwi na Casu Marzu
Abin da ya sa wannan abincin ya fita daban shi ne yana dauke da tsutsotsi.
Wannan na iya sa wa a ji kyama, amma wannan cikwi din dan asalin garin Sardinia, na Italiya na da masoya da yawa.
Ana hada wannan cukwi din ta hanyar hada tsutsar kuda a cikin cukwi din 'pecorino', wani nau'i na cukwi mai kama da cukwi din 'permesan'.
A hankali, kananan tsutsotsi na sa cukwin ya yi laushi yadda idan aka zuba a kwano za a ci, cikinsa ya zama ruwa-ruwa.
Cukwin Casu marzu na da dandano na daban saboda kashin tsutsotsin.
Kafin a ci shi, sai an dauki wasu matakai.
Daga farko, sai kana da hanzarin kama tsutsa- tana iya tsalle tsawon sentimita 15- idan ana cin cukwin.
Abu na biyu shi ne, yana da wuyar samu. Casu marzu ba ya cikin jerin abiinci da Tarayyar Turai ta amince da su, domin haka ba a iya shigo da shi.
Na uku, an bayyana shi a matsayin cukwi mafi hadari a duniya saboda yana iya yin illa ga lafiya.
Wannan haka yake, idan tsutsotsin sun mutu (sai dai idan mutuwa suka yi bayan da aka sa cukwin a firji) saboda wannan na nufin cukwin ya lalace.
Idan aka ci lalataccen cukwin, wannan na iya haifar da ciwon ciki da amai da zawo.
3. Ganyen Rhubarb
Ana amfani da tsinken ganyen rhubarb sosai misali a girke-girken Birtaniya.
Abinci da yawa a Birtaniya na dauke da shi.
Sai dai dole a kula saboda koren ganyen rhubarb na dauke da guba.
Babban abin shi ne yana dauke da sinadari mai guba da ake kira 'oxalic acid', wanda idan aka ci shi da yawa yana janyo tashin zuciya da duwatsun koda.
Ana ci gaba da muhawara kan hadarin ganyen rhubarb saboda yawan sinadarin 'oxalic acid' da ke cikinsu.
Ana samun 'oxalic acid' a jikin tsinkayen, amma ya fi yawa a ganyen.
Sai dai sai idan an ci da yawa ne yake iya kashe mutane, amma gara kar a ci kwata-kwata.
4. Jan wake da waken soya
Ana ganin wake a matsayin abinci mai inganta lafiya, amma akwai wani nau'insa da idan ba a kula ba, yana iya haifar da rashin lafiya.
Jan wake da waken suya na cikin wannan nau'in.
A wani bangare, suna dauke da sinadaran 'protein' da 'vitamin' masu gina jiki.
Amma kuma, danyen wake na dauke da wani irin mai, mai suna 'phytohaemagglutinin' wanda jikin dan Adam ba ya iya sarrafa shi.
Cin sa da yawa na janyo ciwon ciki da haraswa.
Abin farin ciki shi ne dafa waken sosai yana kawar da wadannan abubuwan.
Waken suya kuwa na dauke ne da wani sinadari mai guba mai suna 'trypsin', wanda ke iya hana jikin mutum sarrafa abincin.
Amma idan aka jika wadannan nau'ika na wake a ruwa tsawon awa 12, sannan a tafasa su na kawar da wannan sinadari.
5. Gyadar Miya
Wannan wani nau'i ne na kayan kamshi daga wata bishiya a Indonesiya.
Tana da muhimmanci sosai wajen dafa wasu nau'ukan abinci kamar biskit da kunu.
Baya ga haka, ana amfani da gyadar miya wajen dafa dankali da nama da miya da ganyayyaki.
Sai dai, idan aka sa ta da yawa tana janyo abubuwa da dama: tashin zuciya da daukewar numfashi har ma da suma- da kuma gushewar hankali.
Da wuya, rashin lafiya dalilin cin gyadar miyar (nutmeg) da yawa ya jawo kisa amma yana wahalarwa.
Amma me ma zai sa mutum ya ci kayan kamshi haka da yawa a lokaci guda? To, an dade ana amfani da gyadar miya a wajen gusar da hankali.
Sai dai idan aka yi la'akari da abubuwan da suke jawowa, babu ma amfanin cin gyadar ya wuce kima.