An kashe masu zanga-zanga 106 a Iran - Kungiyar Amnesty

Iran

Asalin hoton, AFP

Gwamman mutane ne ake fargabar sun mutu a kasar Iran tun bayan barkewar zanga-zanga kan karin kudin man fetir ranar Juma'a, in ji ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya.

Mai magana da yawun ofishin ya nemi jami'an tsaro na su daina amfani da karfi fiye da kima da ya hada da amfani da harsashi.

Ya kuma yi kira da gwamnatin Iran ta dawo wa da 'yan kasar Intanet.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce ta samu sahihan rahotanni da ke nuna cewa akalla mutum 106 aka kashe a biranen kasar guda 21.

Gwamnatin Iran dai ta musanta cewa mutanen da suka hau tituna masu zanga-zanga ne.

Shugaba Rouhani ya ce "duk wani dan kasa na da 'yancin yin zanga-zanga wadda ta banbanta da bore."

Har kawo yanzu dai babu cikakken bayani dangane da abin da ke faruwa saboda rufe intanet da aka yi ranar Asabar.

Tun dai ranar Juma'a masu zanga-zanga ke ci gaba da hawa tituna a biranen kasar domin nuna rashin amincewarsu kan karin farashin mai da gwamnati ta sanar za ta yi da kaso 50%.

A ranar Lahadi ne zanga-zangar ta fadada zuwa birane da garuruwa 100, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars News ya sanar.

Akalla masu zanga-zangar sun kona bankuna 100 da shaguna 57 sannan an kama fiye da mutum 1,000.

Shugaba Hassan Rouhani ya ce gwamnati ta yi karin ne domin samar da kudaden da za a bai wa 'yan kasa mabukata.

Jerin takunkuman da Amurka ta kakaba wa ne dai suka jefa kasar cikin wannan yanayi