Zanga-zanga ta barke kan farashin man fetur a Iran

A man fills up his vehicle at a petrol station in Tehran on 15 November 2019

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A karkashin sabon tsarin, an kara farshin man fetur bayan kayyade yawan da ake sayar da shi ga jama'a

Zanga-zanga ta barke a a Iran bayan da gwamnati ta kara farashin man fetur da kimanin kashi 50 cikin 100.

Farashin man fetur ya tashi a daukacin Iran da kashi 50 bayan da aka janye tallafin man.

Dalilin yin haka a cewar gwamnati shine don ta samu kudin da za ta tallafawa marasa karfi.

Cars queue at a petrol station in Tehran on 15 November 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana iya ganin dogayen layin sayen man fetur a Tehran tun ranar Juma'a

Dama Iran na fama da gurguncewar tattalin arziki saboda takunkumin da Amurka ta kakaba mata tun bayan da kasashen biyu su ka yi baram-baram kan shirin nukiliyar Iran.

Mutune biyu sun rasa rayukansu a garuruwan Sirjan da Behbahan kuma gwammai sun jikkata.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa an yi artabu da jami'an tsaro a lokacin da masu zanga zangar suka yi yunkurin kona wata ma'ajiyar man fetur a ranar Juma'a.

Wasu garuruwan da rikicin ya shafa sun hada da babban birnin kasar wato Tehran da Kermanshah da Isfahan da Tabriz da Karadj da Shiraz da Yazd da Boushehr da kuma Sari.

A yawancin biranen masu boren sun rufe hanyoyi ta yin amfani da ababen hawansu don rufe hanya.

Protests have also spread to the capital Tehran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zanga-zangar ta bazu zuwa babban birnin kasar Tehran

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a internet ya nuna wasu gine gine na ci da wuta da suka hada da bankuna.

Shugaba Hassan Rouhani ya bayyana cewa kashi 75 na yan kasar na cikin matsi, kuma karin farashin zi tafi ne kacokam kan tallafa musu don ganin sun samu saukin rayuwa.

Iran na daga cikin kasashen da ke samar da man fetur a duniya, kuma ta na sayar da man na ta da sauki sosai.

To sai dai takunkumin da Amurka ta kakaba mata ya dagula al'amura a kasar, da suka hada da kasa samun damar shigo da injinonan da mahakar man fetur din kasar ke bukata.

Bugu da kari, tattalin arzikin ta ya lalace, yayin da darajar kudin ta ta yi kasa,dalilian da suka haifar da hauhawar farashin ababen more rayuwa.