Hillary Clinton ta ce an matsa mata ta tsaya takara 2020

Lokacin karatu: Minti 2

Hillary Clinton ta ce tana fuskantar matsin lamba ta fito takarar shugaban kasa domin kalubalantar Shugaba Donald Trump na Amurka a fadar White House.

Clinton, wadda Trump ya doke a 2016 ba ta bayyana cewa ba za ta karbi kiran ba, kamar yadda ta shaida wa BBC cewa "Ba za a taba yanke kauna ba."

Clinton mai shekara 72, ta ce a kullum takan yi tunanin irin shugabar da za ta kasance idan da ta doke Trump a zaben 2016.

'Yan takara da dama ne daga bangaren Democrats ke son fafata wa da Trump a zaben 2020.

An tambayi Clinton ko za ta sake tsayawa takara, kuma ta amsa cewa; "Tabbas zan yi tunani akai, nakan yi tunani a kullum, yadda zan iya da kuma hanyoyin samun nasara da kalubalen da ke gabana"

"Amma a yanzu haka da nake zaune da kai a nan muna tattaunawa, ba ya cikin tsarina."

Mrs Clinton ba ta yi karin bayani kan ko waye ke matsa mata lambar tsayawa takara a karo na ukun ba.

Hirar wacce aka nada a Landan na zuwa ne a yayin da take neman a san wani littafi mai suna "The Book of Gutsy Women," wanda suka rubuta shi ita da 'yarta, Chelsea Clinton.

Har yanzu dai ba a san ko wane ne zai yi nasara a jam'iyyar Democrat ba, da zai kasance shi ne wanda zai fafata da Mista Trump a watan Fabrairu, don ana ci gaba da kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta jihohi.

Wa zai fafata da Trump a 2020?

Akwai sauran shekara daya kafin ranar zaben, amma tuni aka fara fafatwa don zaben wanda zai kalubalanci Mista Trump daga jam'iyyar Democrat.

Kuri'un farko-farko da aka kada na nuna cewa Ms Elizabeth Warren da Mista Joe Biden ne a kan gaba, yayin da Mista Bernie Sanders ma yake tashe sosai.

Sai dai yawancin sauran masu takarar ba a san su ba a sauran wurare kamar yadda aka san su a Birnin Washington.