Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyar IS ta yi sabon shugaba
Kungiyar IS ta tabbatar da mutuwar jagorata Abu Bakr al-Baghdadi kuma an bayyana magajinsa.
Kungiyar ta bayyana sunan Abu Ibrahim al-Hashemi al-Qurayshi a matsayin sabon jagoransu kuma "Khalifanta."
Wasu dakarun musamman na Amurka ne suka kai wa al-Baghdadi farmaki a gidansa da ke arewa-maso-yammacin Syria a karshen makon jiya.
Daga nan ne kuma sai jagoran IS din ya tsere zuwa wata mabuya ta karkashin kasa, inda ya kashe kansa.
A shekarar 2014 ne aka ayyana marigayin a matsayin jagoran IS lokacin da kungiyar ta karbe iko da wasu yankuna a kasashen Iraki da kuma Syria.
A wani sakon sauti, IS ta tabbatar da mutuwar kakakin kungiyar Abu al-Hasan al-Muhajir - wanda aka kashe a wani farmaki na daban, bayan wani hari da dakarun Amurka da hadin gwiwar dakarun Kurdawa suka kai masa.
Wasu suna ganin al-Muhajir wanda dan asalin Saudiyya ne a matsayin wanda aka tsara zai gaji al-Baghdadi.
Sabon kakakin kungiyar Abu Hamza al-Qurayshi ya yi kira ga Musulmi da su yi biyayya ga Abu Ibrahim al-Hashemi.