Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Tafiye-tafiyen Buhari na da tasiri kan Najeriya'
A Najeriya, masana sun fara tofa albarkacin bakinsu game da tafiye-tafiyen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi zuwa ketare, wadanda jam`iyyar hamayya ta PDP ke zargin cewa ba su da wani amfani.
A ranar Litinin ne dai shugaban kasar ya wuce kasar Saudiyya, kwana biyu bayan dawowarsa daga kasar Rasha.
To sai dai jam'iyyar adawa ta PDP ta ce ba ta gani a kasa ba, duk da cewa bangaren gwamnati na cewa Najeriya na cin gajiyar wadannan tafiye-tafiyen.
Masana kimiyyar siyasa irin su Dr Abubakar Kari, na yi wa tafiye-tafiyen na shugaba Buhari da ke cike da takaddama wani irin kallo.
Latsa wannan alamar lasifikar domin sauraron Dr Kari a hirarsa da Ibrahim Isa: