Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasashen Yamma na yi wa Afirka mulkin mallaka - Putin
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya bayyana cewa kasarsa za ta iya taimaka wa nahiyar Afirka ba tare da wasu sharudda ko yarjejeniya ba.
A wata tattaunawa da Mista Putin ya yi da kamfanin dillancin labarai na TASS ya bayyana cewa ''mun ga yadda wasu Kasashen Yammaci ke matsa lamba da takurawa ga gwamnatocin kasashen Afirka masu iko.
''Suna amfani da irin wadannan hanyoyi ne domin dawo da karfin da suke da shi irin na lokacin mulkin mallaka, wanda hakan suna yi ne da niyyar samun riba da kuma cutar da tattalin arzikinsu.''
Ana sa ran Rasha za ta tattauna da shugabannin kasashen Afirka 47 tsakanin 23 zuwa 24 ga watan Octoba.
Mista Putin ya bayyana cewa dangantakarsa da Afirka ta kara karfi inda ya bayar da misali da bangaren inganta sojoji inda ya ce kasar na samar da makamai ga kasashen Afirka kusan 30 a halin yanzu.
Rwanda na daga cikin kasashen da ke da dangantaka mai karfi da Rasha.
A 'yan kwankin nan, gwamnatin Rwanda ta bayar da dama domin yin wata yarjejeniya da Rasha domin inganta amfani da makamashin nukiliya amma za a yi amfani da nukiliyar ta ''hanyar zaman lafiya,'' kamar yadda wata jaridar Gabashin Afirka ta ruwaito.
Za a yi amfani da nukiliyar wajen habaka aikin gona da samun wutar lantarki da kuma kare muhalli, in ji rahoton.