Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masana kimiyya na bincike kan abin da ke jawo cutar kansa
Masu bincike kan cutar kansa daga Birtaniya da Amurka na kokarin hada hannu domin gano alamomin farko da suke nuna mutum na dauke da cutar kansa kafin cutar ta yi karfi.
Suna kokarin ''kirkirar'' cutar kansa a dakin gwaje-gwaje domin ganin ko ya cutar ke kasancewa a ranar farko.
Wannan na daya daga cikin bukatun kungiyar ''International Alliance for Cancer Early Detection'' wadda kungiya ce da ke bincike kan kansa.
Kungiyar ta ce hada hannu da sauran masu bincike domin gano cutar da sauri abu ne wanda zai amfanar da marasa lafiya.
Kungiyar bincike ta ''Charity Cancer Research UK'' ta hada hannu da Jami'ar Cambridge da Manchester da University College ta Landan da kuma jami'o'in Stanford da Oregon domin kara wa juna sani kan kimiyya ta wannan bangaren.
An zo wurin
Masu binciken na kokarin yin gwajin jini da numfashi da fitsari domin sa ido kan marasa lafiya masu yiwuwar kamuwa da cutar kansa, da kuma kara inganta fasahar daukar hoton jaririyar cutar kansa kafin ta habaka.
Amma masu binciken sun bayyana cewa hakan tamkar neman allura ce cikin ruwa wanda za a iya shafe shekara 30 ana yi.
Dakta David Crosby wanda shi ne shugaban cibiyar binciken gano cutar kansa da wuri ta Birtaniya ya ce ''babbar matsalar ita ce ba za mu iya gane lokacin da kansa ke farawa a cikin jikin dan Adam ba.
''Zuwa lokacin da za mu gano cutar ta riga ta shiga jiki sosai.''
Masu bincike kan cutar kansa daga Manchester da kuma Birtaniya misali, na kokarin gwajin naman mama da habaka shi domin ganin ko za su iya gano alamomin farko na cutar kansa.
Har wa yau, masana kimiyya sun bayyana cewa bincike wajen gano cutar kansa da wuri bai fadada ba, masu binciken ba su cika samun nasara wajen gano cutar ba.
Dakta Cosby ya ce hada hannu da za a yi zai kawo sauyi matuka ta bangaren kiwon lafiya, wannan zai sa a matsa daga kona cutar kansa zuwa kokarin shawo kanta a matakin farko da kuma maganceta.
Kididdiga ta nuna cewa kashi 98 cikin 100 na masu kansar mama suna rayuwa shekara biyar ko kuma fiye idan aka gano cutar a matakin farko, idan aka hada da kashi 26 cikin 100 na wadanda ake ganowa a mataki na hudu.
Amma a halin yanzu, kusan kashi 44 na masu kansar mama ana gano cutar a jikinsu ne a matakin farko.
A Birtaniya, an kebe lokaci na musamman domin gwaji ga masu cutar kansar mama, da kansar ciki da kuma ta mahaifa idan mutane suka kai wasu shekaru.
Sai dai a halin yanzu, babu kayan gwaje-gwaje na kansar tumburkuma da ta huhu da koda da ta mafitsara wanda hakan na nufin yiwuwar rayuwa ga masu dauke da ita na da wahala.
Farfesa Mark Emberton ya bayyana cewa kirkiro nau'ura mai daukar hoton jikin mutum domin binciken kwakwaf wato MRI wata hanya ce ta maye gurbin wasu hanyoyi na gano cutar kansa musamman ta mafitsara.